An Kaddamar Da Nuna Shirye-shiryen Fina-finai Da Na Talabijin Na “Gano Kyawun Xinjiang” A Kasashen Waje A Hukumance

- Advertisement -

An Kaddamar Da Nuna Shirye-shiryen Fina-finai Da Na Talabijin Na “Gano Kyawun Xinjiang” A Kasashen Waje A Hukumance

Daga CRI Hausa

Da karfe three na yammacin yau Alhamis ne aka gabatar da shirin “Fiye Da Tsaunukan Tianshan” da Babban Rediyo da Talibijin na kasar Sin wato CMG ya tsara cikin harshen Larabci, a gidan talibijin na kasar Lebanon. Wannan alama ce dake kaddamar da ayyukan nuna shirye-shiryen fina-finai da na talabijin masu taken “Gano Kyawun Xinjiang” a kasashen waje a hukumance.

Za a gudanar da ayyukan daga tsakiyar watan Mayu har zuwa karshen watan Yuli. Za a nuna shirye-shiryen fina-finai da na talabijin na “Gano Kyawun Xinjiang” a wasu manyan kafofin yada labarai na kasashe sama da goma, ciki har da Masar, Turkiyya, da Lebanon, da Indonesia, da Malaysia, da Najeriya, da Kenya, da kuma Tanzania.

Wurare masu ni’ima, da abinci mai dadi, da kuma kyakkyawan yanayin zaman rayuwam, su ne suka kasance jigon shirye-shiryen. Kana za a watsa shirye-shiryen cikin harsuna bakwai, ciki har da Turancin Ingilishi Larabci, da harshen Turkiyya, da harshen Indonesia, da harshen Swahili, da harshen Hausa da dai sauransu, wadanda CMG ya fassara, ciki har da shirye-shiryen telebijin na “Fiye da Dutsen Tianshan”, da “Sin daga Sama: Xinjiang”, da “Dandanon Xinjiang”, da fim na “Jaruma Mina”, da cartoon na “Kela da Mayi” da dai sauransu, ta yadda masu kallo daga kasashe daban daban, za su kara fahimtar kyawawan wurare, da abincin masu dadi, wadanda ba za’a iya mantawa da su ba, da kuma zaman rayuwa mai dadi da jituwa dake akwai a jihar Xinjiang. (Zainab)

- Advertisement -