An Kaddamar Da Bukukuwan Watan Bunkasa Sayen Kayayyaki Da Na Sayayya Na Ranar 5 Ga Watan Mayu Na Shanghai

0
53

An Kaddamar Da Bukukuwan Watan Bunkasa Sayen Kayayyaki Da Na Sayayya Na Ranar 5 Ga Watan Mayu Na Shanghai

Daga CRI Hausa

An kaddamar da bikin bunkasa sayen kayayyaki da kuma bikin sayayya na Shanghai na ranar 5 ga watan Mayu, da yammacin ranar 1 ga watan Mayu bisa taken “Extra amfani da kayayyaki da kyautata rayuwa”.

Ma’aikatar kula da cinikayya da rukunin kafafen yada labarai na kasar Sin CMG da gwamnatin birnin Shanghai ne suka kaddamar da bukukuwan a cibiyar nune-nune ta Shanghai.

Bikin ya kuma samu halartar sakataren kwamitin JKS na birnin Shanghai Li Qiang, da ministan kula da cinikayya Wang Wentao, da kuma shugaban rukunin kafafen yada labarai na kasar Sin CMG, Shen Haixiong.

Da yake jawabi, shugaban CMG Shen Haixong, ya jadadda cewa, tattalin arzikin kasar Sin na tafiya yadda ya kamata, bisa juriya mai karfi da karuwar sayen kayayyaki. Ya ce karuwar sayayya a cikin gida ne ke ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar cikin shekaru da dama a jere. Ya kara da cewa, a matsayinsa na kafar yada labarai ta rediyo da talabijin, CMG ya dage wajen taimakawa farfadowar sayayya da samar da damarmaki daga mabanbantan hanyoyi domin taimakawa samar da wani sabon tsarin ci gaba.

Har ila yau, ya ce a bara, CMG da ma’aikatar kula da harkokin cinikayya, solar tsara wasu shirye-shirye kamar na watan bunkasa sayen kayayyaki na farko, wanda ya karawa masu sayayya kwarin gwiwa yayin da ake fuskantar annobar COVID-19. A cewarsa, a sabon zamani na sayayya, CMG zai ci gaba da amfani da karfin yada labarai domin taimakawa watan na bunkasa sayayya, da taimakawa bikin sayayya na 5 ga watan Mayu na Shanghai, da bunkasa gina cibiyar sayayya ta kasa da kasa a Shanghai. Bugu da kari, zai taimakawa shanghai samun ci gaba mai matukar inganci da ingantaciyar rayuwa, da gina birni mai tsarin gurguza na zamani dake da tasiri ga duniya. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)

What's On Your Mind?