An Harhada Wasu Tsofaffin Littattafan Addinin Musulunci A Kasar Habasha

0
54

An Harhada Wasu Tsofaffin Littattafan Addinin Musulunci A Kasar Habasha

Shafin yada labarai na Al’ain ya bayar da rahoton cewa, Hassan Muhammad Kawo, wani mai bincike ne a kasar Habasha, wanda ya samu damar harhada wasu tsofaffin littattafai na addinin Muslunci da tarihinsu ke komawa zuwa ga karni na 14 miladiyya.

Ya ce ba abin mamaki ba ne idan an samu tsoffin littafai na addinin Muslunci a cikin kasar Habasha, domin kuwa ita ce kasa ta farko da musulmi suka nufa a lokacin da suka yi hijira tare da umarnin Manzon Allah (SAW) daga Makka.

Baya ga haka kuma wannan ya nuna tsahuwar alakar da ke akwai tsakanin al’ummar wannan kasa da kuma msuilmi, inda yanzu haka akwai tsoffin littattafai na addinin Muslunci da aka rubuta daruruwan shekaru masu yawa da aka samu a kasar habasha, kuma ana ajiye da su a  babban dakin ajiye kayan tarihi Bilal Al-Habashi da ke birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar.

What's On Your Mind?