Hotuna: Girman kai rawanin tsiya: An hango gwamnan Kwara yana yankar ciyawa

0
47

Gabannin komawa makaranta a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, ya shiga sahun al’umman Oloje wajen yanke ciyawa a makarantar sakandare na Mount Camel.

Gwamna AbdulRazaq wanda ya wallafa hotunan a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa idan gwamnati ta ajiye wani aiki a wani gari, hakkin mutanen garin ne su kula da shi tamkar nasu.

An hango gwamnan Kwara yana yankar ciyawa

Ya ce ya aikata hakan ne domin karfafa wa mutane gwiwar kula da gine-ginen gwamnati da ke a yankunansu. Gwamnan ya bayyana cewa:

“Kasancewana a Oloje a yau shine domin nuni ga cewa babu wanda ya fi karfin shiga aikin gayya; ya kamata mu taimaki kanmu.”

A cewarsa, gwamnati na fama da karancin kudi saboda haka ba za ta iya jurewa ba.

Hotuna da bidiyon motar N460 miliyan da Dino Melaye ya siya

Saboda haka ya yi kira ga al’umma da su hada hannu su bayar da taimakon da za su iya, domin ganin an tsaftace muhalli don gudun afkuwar annobar muhalli.

A wani labari na daban, Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Alhamis ya sanar da sakin fursunoni 25, rage wa’adin wasu ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai.

Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin jawabinsa na bikin ranar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci.

https://twitter.com/RealAARahman/standing/1312451929037971457?ref_src=twsrcpercent5Etfwpercent7Ctwcamppercent5Etweetembedpercent7Ctwtermpercent5E1312451929037971457percent7Ctwgrpercent5Eshare_1&ref_url=httpspercent3Apercent2Fpercent2Fhausa.legit.ngpercent2F1371581-girman-kai-rawanin-tsiya-an-hango-gwamnan-kwara-yana-yankar-ciyawa.html

 

What's On Your Mind?