An Hana Magoya Bayan Chelsea Da Manchester City Zuwa Kallon Wasan Karshe

- Advertisement -

An Hana Magoya Bayan Chelsea Da Manchester City Zuwa Kallon Wasan Karshe

Daga Abba Ibrahim Wada

An hana magoya bayan Chelsea da Manchester City zuwa kasar Turkiyya domin kallon wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai tsakanin kungiyoyin biyu saboda annobar cutar Korona.

Sakataren harkokin sufuri na Burtaniya Grant Shapps ne ya sanar da hakan, bayan sanya sunan Turkiyyan cikin jerin aasashen da aka haramta zuwa saboda yawan masu kamuwa da cutar a kasar.

Wasa mafi mahimmanci a Turai wanda za’a buga a birnin Istanbul a ranar 29 ga watan Mayu shine wanda za’a buga ranar 29 ga wata tsakanin manyan kungiyoyin biyu da suke hamayya da juna.

Schapps ya ce kasashen da aka sanya sunansu cikin bakin littafi saboda korona ba za a je cikinsu ba sai da wani kwakwaran dalili kuma ya kara da cewa gwamnati dai-dai take da daukar nauyin wasan a yi shi a Ingila.

Schapps ya ce hukumar kwallon kafa ta Ingila na tattaunawa da hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai, Uefa kan yadda za’a koma da wasan Burtaniya, amma hukuncin haka na hannun Uefa.
“Burtaniya na da tsari mai kyau na bibiyar wannan cutar ta yadda za ta iya daukar nauyin buga wasan tare da ‘yan kallo, mune wurin da ya kamata a yi wasan saboda kula da lafiyar mutane,” in ji shi.
Ya kara da cewa “Dan haka kofar mu a bude take domin yin hakan, amma dai ko me za a yi Uefa ke da hukuncin karshe sai dai ganin cewa duka kungiyoyin na Ingila ne shi yasa muke neman yadda za muga an bar mu.”
Tuni da kungiyar kwallon kafa ta Aston billa ta bayar da damar cewa zata amince a buga wasan karshen a filin wasanta na billa Park dake birnin Birmingham dake Ingila sannan kuma ana zaton za’a iya kai wasan filin wasa na Wembley dake London.

- Advertisement -