An hallaka mutum 80 yayin rikicin ƙabilanci

0
60

Likitoci a Sudan solar ce an kashe mutane fiye da tamanin a cikin kwanaki biyu da aka kwashe ana arangama tsakanin ƙabilun da ke gaba da juna a yankin Darfur.

Wasu ɗaruruwan kuma solar jikkata yayin hargitsin a El Geneina.

Haka kuma an kai hari wani sansanin mutanen da suka rasa matsugunansu a yayin mummunan tashin hankali tun lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan Oktoban da ya gabata.

Dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya solar fara janyewa daga yankin na Darfur a farkon wannan watan.

An hallaka mutum 80 yayin rikicin ƙabilanci

Rahotannin solar ce rikicin ya fara ne lokacin da wani mutumi ya daɓawa wani balarabe wuƙa tare da kashe shi, abin da ya janyo musayar wuta tsakanin ƙabilun mutanen biyu.

Yahoo Boy Arrested With His Girlfriend’s Corpse In Delta

Gwamnatin ƙsar dai na aikewa da sojoji zuwa yankin don kare fararen hula.

A rikicin baya-bayan nan, an ƙona ƙauyuka da dama, da kasuwanni da shaguna sannan aka sace abubuwan da ke ciki, a cewar shugaban ƙungiyar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya.

“Ci gaba da rikici a yankuna da dama na Darfur ya haddasa ƙaruwar mutanen da ke rabuwa da matsugunansu, da tsayawar harkokin noma, da ma ƙruwar waɗnda ke mutuwa.

Kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya tana neman tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir, wanda aka hambarar daga kan mulki a bara, inda take zarginsa da aikata laifukan yaƙi da kisan kare-dangi a yankin.

Yanzu haka ana shari’ar tsohon shugaban kasar mai shekara 76 a gaban wata kotu da ke Khartoum bisa alaƙa da juyin mulkin soji na shekarar 1989.

What's On Your Mind?