An Gano Wata Sabuwar Duniya Cike Da Tsirran Ganyen Wiwi

0
85

An Gano Wata Sabuwar Duniya Cike Da Tsirran Ganyen Wiwi

Hukumar bincike a sararin Subhaana “NASA” ta bayyanar da ganin wata sabuwar duniya, wadda ke cike da tsirran ganyen wiwi. Wannan binciken ya ba wa duk daukacin masu gudanar da binciken mamaki, sun ce duniyar d637Z-43 an gano ta ne a lokacin da aka yi amfani da na’urar hange ta hukumar.

Sun kara da cewar wannan na iya zama daya daga cikin irin wasu duniyoyi, da ba su bayyana ba, a cewar masana na NASA, sun kuma iya gano cewar, akwai wadatacciyar iskar gas, a duniyar wanda dan’adam kan iya rayuwa a wajen.

Maryam Malika Ta bayyana Matsayin Aurenta a Yayin cike Form din zama cikakkiyar Jaruma a Kannywood

Masanan dai sun kara da cewar, samun ganyen wiwi a nahiyar na iya zama wani abu da zai sa mutane, su zurfafa bincike a kan ganyen. A tabakin Mista Dabid Charbonneau, Malami a tsangayar binciken rayuwar wata da taurari, na jami’ar Harbard, ya ce mafi aksarin matasa suna son ganyen wiwi, don haka akwai bukatar matasa su tashi tsaye wajen bincike, don gano alfanun ganyen ba kawai su dinga shan sa har ma ya kauda musu da tunanin ba.

What's On Your Mind?