An Cafke Ma’aikacin Gidan Yari Bisa Zargin Shigar Da Kwayoyi Fursunan Kano

0
86

An Cafke Ma’aikacin Gidan Yari Bisa Zargin Shigar Da Kwayoyi Fursunan Kano

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Hukumar dake lura da gidajen gyaran hali ta Jihar Kano ta ce ta kama kunshi shida na tabar wiwi da nauyinsu ya kai kilogiram four.5 da kuma wayoyin hannu takwas da aka yi kokarin shigarwa tare da wadanda aka yanke wa hukuncin kisa gidan.
Haka kuma an samu nasarar damke daya daga cikin ma’aikatan gidan gyaran halin da wani babban dilan miyagun kwayoyi bisa zarginsu da aikata hakan inda aka mika su ga hukumar da ke yaki da hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi ta NDLEA.
Wata majiya daga gidan gyaran hali ta Kurmawa da ke Jihar Kano, ta shaida wa MOBILIZED9JA A Yau cewa, a ranar alhamis da ta gabata  wani ma’aikacin gidan gyara halin, ba tare da sanin ana bibiyarsa ba ya hadu da wani dilan kwaya wanda ya kawo wasu kaya tare da wayar hannu kirar Android domin kai wa wasu wadanda ke jiran hukuncin kisa a gidan gyaran halin na Kurmawa.

“Matashin ma’aikacin da aka dauka aiki shekaru biyu da suka shude, mai suna Aminu Ibrahim ya hadu da wani dilan kwaya a kusa da gidan Makama sannan ya karbi kayan tare da kwayoyin, kuma kowacce wayar hannu na dauke da sunan wanda za’a bai wa domin gudun kuskuren bai wa wani.” In ji majiyar.
Sakamakon kwace wadannan kaya ne ya fusata wasu daurarru wadanda suka sa ran karbar wadannan kayayyaki, suka nemi lallai sai a basu kayan da aka kama nan ta ke sannan kuma dole a saki wadanda aka kama na kokarin shigar da kayan gare su.
Majiyar ta ci gaba da cewa shugaban, wadanda ke jiran hukuncin kisan, ya yi barazana ga jami’an gidan gyaran halin cewar, idan ba’a saki kayan da aka kama masu ba, babu sauran zaman lafiya a gidan.

Tun daga sauyawa shugaban wannan gida wurin aiki makonni uku da suka gabata daga Wudil domin karbar aiki tun da jami’in dake lura da wannan gida ya tafi karin ilimi na watannin biyu.
A ranar da ya dawo aiki, ya fahimci lallai tarbiyyar gidan ta sauya baki daya, wanda har ta kai wasu ma’aikatan gidan na hada baki da daurarrun da suke jiran hukuncin kisa domin shigar masu da wayoyi da kayan da aka haramta shiga da su.
Kasancewar ya kware matuka da sanin halayyar gidan tsawon shekara 15 da ya yi yana aiki da su, ya sa yanzu ya samar da tsarin bibiya tare da lura da dukkan harkokin daurarrun da ke jiran hukuncin kisa. Wannan ta sa aka samu faruwar wannan al’amarin da yammacin ranar alhamis.
Sakamakon gogewar mai lura da gidan yanzu da yawa daga cikin ma’aikatan, na iya magance tarzoma ba tare asarar ran daurarru ko ma’aikatan gidan, ko kuma yin asarar dukiyar gwamnati ba.
Zuwa lokacin da nake maganar nan da ku, ana ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo wadanda ke hada baki da daurarrun da kuma shigo da kayan da aka haramta shigowa da su cikin gidan gyaran halin.

Mai Magana da yawun hukumar gidan gyaran halin na Jihar Kano DSC Musbahu kofar Nasarawa ya tabbatar da kame dilan kwayar da kuma ma’aikacin gidan gyaran halin a ranar Asabar da ta gabata. Ya ce tuni aka mika wadanda aka kama din ga hukumar hana sha da fautacin miyagun kwayoyi ta jihar a ranar juma’a, sai dai bai yi karin haske kan lamarin ba.

What's On Your Mind?