An Bukaci Musulmi Su Kara Kaimin Ibada A Goman Karshe Na Watan Ramadan

0
61

An Bukaci Musulmi Su Kara Kaimin Ibada A Goman Karshe Na Watan Ramadan

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Wani Malamin Addinin Islama da ke zaune a Abuja, Imam Yahya Al-Yolawi, ya bukaci Musulmai da su kara Ibada da bautar Allah don kara samun sakamako a cikin kwanaki 10 na karshen Ramadan.

Al-Yolawi, wanda shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a na Space 10 Garki Abuja, ya ba da wannan shawarar ne a lokacin da yake gabatar da hudubar jumma’at mai taken, “Kwanaki Goman karshe na Ramadan,” a ranar Juma’a a Abuja.

Ya bayyana cewa kwanaki 10 na karshe na Ramadan ranaku ne na musamman a rayuwar kowane Musulmi, ya kara da cewa su ne ranakun da suka fi falala a cikin watan Ramadan. A cewar sa, malamai solar ce, duk da cewa an gafarta wa Annabi zunubansa, hakan bai hana shi ya dukufa ga yin ibada cikin wadannan kwanaki 10 na karshe ba, da fatan samun kusanci ga Allah.

“Manzon Allah (SAW) ya kasance yana daura dammara kuma domin yin tsayin daka kan yin addu’o’i tsawon dare, kuma ya kan umartar iyalansa da su tashi tsaye domin raya dare wajen yin nafilfili cikin wannan lokaci.

“Ga Musulmai, kwanaki 10 na karshe su zama lokaci ne na kammala azumin mutum da kuma guje wa duk abin da zai iya karya shi. Haka nan lokaci ne na ba da karin sadaka da sasanta rikice-rikice da yafe wa juna.

“Ya kamata mu himmatu don neman babban dare wato Lailatulkadri, daren iko wanda ke buya a cikin daya daga cikin darare 10 na karshen Ramadan, musamman a cikin dararen mara adadi. “Yin addu’a awannan daren ya fi watanni 1,000 ko shekaru 83 na ibada watanni shida. Allah Ya taimake mu mu ga wannan dare, ”ya yi addu’a.

Shehin malamin ya shawarci musulmai da su kiyaye sallolin tsakiyar dare, sannan ya kara da cewa duk wanda ya yi sallah da daddare a cikin Ramadan saboda imani da kuma fatan samun lada, za a gafarta masa zunuban da ya gabata.

What's On Your Mind?