An Bukaci Gwamnatin Buhari Ta Dakile Hauhawar Farashi Kayan Masarufi

0
83

An Bukaci Gwamnatin Buhari Ta Dakile Hauhawar Farashi Kayan Masarufi

Daga Idris Umar Zariya

Sheik Ashara shi ne Sarkin malaman karamar hukumar Makarfi kuma mataimakin shugaba Fitoyanul Islam na jihar Kafuna kuma yana daya daga cikin jagororin shugabanin babbar kasuwar Makarfi a yanzu haka.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake garin Makarfi ya ce, dagawar farashin kayan masarufi a lokacin azumi rashin tausayi ne, ya ce, yakamata ne gwamnati da ‘yan kasuwa su hadansu guri guda don samun daidaituwar farashi wanda hakan zai kawo albarka a cikin kasa kuma hakan na kauda masifu iri daban daban.

Sheshin Malamin ya nuna takaicinsa recreation da halin da wannan gwamnatin ke ciki har yake tambaya anya shugaban kasa Muhammadu Buhari yasan halin da talakan da ya zabeshi yake ciki kuwa?
Ya ce, su a saninsu Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne mai adalci da saninin ya kamata ya ce, kowa ya san mulkinsa na baya babu wani dankaruwa da ya isa ya kara farashin kaya ba tare da izinin gwamnati ba.

Ya ce akan idansu gwamnatin Muhammadu Buhari ta bada umurnin cewa duk wanda ya kara kudin daya wuce misali gwamnati za ta sanya jami’an tsaro su rabawa jama’ar gari kayan bisa farashin da gwamnati ta sani ya ce, to yanzu meke faruwa da shugaban kasa ne?
Tuni shehin ya ce, wajibi ne shugaban kasa yasan da cewa duk talakan da ya mutu da yunwa a mulkinsa alhalin akwai hanyar da za a iya biya masa bukatarsa to akwai hadarin gaske a ranar gobe kiyama.

Ya ce, shugaban kasa ya yi wa Allah ya yi wa Annabi yasa baki akan tsadar kayan masarufi a kasuwanni musammnan lokacin azubi.

Sheshin ya kwadaitar da masu hannu da shuni cewa duk wanda ya ciyar da mai azumi a watan Ramadana Allah zai masa tanadi mai girma ranar gobe kiyama.
Haka-zalika malamin ya kara da cewa duk wanda ya cutar da mai azumi a watan Ramadana Allah na hushi da hakan.

Don haka ne ma Shehin malamin ya yaba wa Sheik Jamilu Albani Samaru babban darakta a hukumar kula da sha’anin addini na jihar Kaduna bisa yin kurin da ya yi na kokarin hadakan ‘yan kasuwa don daidaita farashin kaya a lokacin azumi a fadin jihar Kaduna duk da yake shehin malamin ya koka ganin yadda aka ki bashi hadin kai da goyan baya tare da nuna son kai a cikin lamarin sai ya ce, Allah ya sakawa Sheik Jamilu Albani Samaru da kokarin kawo gyara.

karshe sheshin malamin ya yi fatan yadda aka fara azumin lafiya Allah yasa a gama lafiya.

 

What's On Your Mind?