An Bukaci Gwamna Buni Ya Gina Masana’antun Sarrafa Tumatir Da Shinkafa

0
64

Mukaddashin shugaban karamar hukumar Bade (DPM) a jihar Yobe, Alhaji Adamu A. Dagona ya bukaci Gwamna Mai Mala Buni ya duba yuwuwar kafa masana’antun sarrafa tumatir da shinkafa a garin Gashuwa da ke jihar bisa la’akari da yadda garin ya kasance cibiyar noma tumatir da shinkafa a jihar kana domin bunkasa tattalin arziki, kudin shiga da
samar wa matasa aikin yi.

Alhaji Dagona ya bayyana hakan a sa’ilin da Gwamna Buni yake dora harsashen ginin kasuwar zamani a garin na Gashuwa- shalkwatar karamar hukumar Bade makonin da suka gabata.

An Bukaci Gwamna Buni Ya Gina Masana’antun Sarrafa Tumatir Da Shinkafa

Ya ce garin Gashuwa cibiya ce ta noman rani, wadda ta dade tana janragamar akalar noma isashen amfanin gona da ake kai shi a kowane lunguda sakon kasar nan. Ya kara da cewa, “musamman irin yadda manoman musu ka shahara wajen noma shinkafa da tumatir mai yawan gaske, wanda ya dace ace akwai masana’antu a wannan yanki don bunkasa su.”

Shugaban karamar hukumar, ya kara da sanar da cewa, baya ga wadannan, yankin ya shahara wajen kamun kifi, noman albasa, karas, tattasai, alkama, da sauran amfanin gona wadanda ake safarar su zuwa sassan kasar nan daban-daban.

“Bugu da kari kuma, gina wannan sabuwar kasuwa ta zamani da gwamnatin jihar Yobe take, a Gashuwa za ta taimaka wajen zaburar da matasan mu fantsama gadan-gadan ga harkokin kasuwanci daban-daban, wanda hakan zai rage matsalolin rashin aikin yi da fatara a wannan karamar hukuma.”

Bidiyo: Saurari Wayar Bosho Da ‘Yan Boko Haram Bayan Yayi Wani Film Inda Yace Ya Iya Hada Bom

A hannu guda, Alhaji Dagona ya ce ko shakka babu wadannan kyawawan manufofi na gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni wajen aikin gina sabuwar kasuwar zamani a garin Gashuwa, zai habaka harkokin ci gaban tattalin arziki a karamar hukumar da ma a jihar baki daya. Ya ce, saboda yadda garin yake cike da manyan yan kasuwa, kuma hakan zai kara musu kwarin gwiwa da karsashi a kasuwancin su.

“Haka kuma, gina wannan sabuwar kasuwa ta zamani, ya zo a lokacin da ya dace saboda kasuwar da ake da ita garin ta dade shekaru aru-aru kuma ta yi wa yan kasuwar kadan.”

“A gefe guda kuma, ta hanyar samun cikakken goyon bayan gwamnatin jihar Yobe hadi da shugabanin bangarori a wannan karamar hukuma ta Bade, mun yi abin a zo a gani wajen yi wa al’umma ayyukan ci gaba, wadanda su ka kunshi tona rijiyoyin burtsatse, gyara wasu da dama, aikin yashe magudanun ruwa tun kafin damina ta shigo, don dakile matsalar ambaliyar ruwa, da sauran muhimman ayyukan da mu ka aiwatar ga jama’a.”

A karshe Alhaji Adamu Dagona ya yaba dangane da kyawawan kudurori da manufofin gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ga al’ummar jihar Yobe tare da kula ta musamman ga jama’ar karamar hukumar Bade, halin dattakon da
ba za su taba mantawa dasu ba, har abada.

What's On Your Mind?