An Bukaci Al’ummar Legas Da Su Rungumi Akidar Zaman Lafiya

0
76

An Bukaci Al’ummar Legas Da Su Rungumi Akidar Zaman LafiyaBabban shugaban kasuwar Mile 12 ‘Worldwide market’ a Legas, Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam Dallatu na Egbaland a jihar Ogun ya shawarci al’ummar kasar nan da su cigaba da bayar da gudummawarsu wajen kawo zaman lafiya a kasar nan baki daya.

Shugaban kasuwar ya yi wannan tsokacin ne a Katsina yayin da ya ziyarci garin Tsiga domin gudanar da taron nadin sarautar tsohon shugaban kasuwar ta Mile 12, Alhaji Haruna Muhammad Tamarke mai dankalin turawa a matsayin magayakin Jarman Katsina da kewayenta. Taron nadin sarautar ya gudana ne a harabar fadar mai girma Jarman Katsina Hakimin tsiga a cikin jihar Katsina a satin da ya gabata.

Tsohon Gwamna Legas, Tinubu babu lafiya, an fitar da shi zuwa wani asibitin waje

A bayanin sa, Dallatun ya bayyana cewa wajibi ne ga dukkan ‘dan kasa na gari da ya yi dukkan wani abu dai zai kawo wa kasar sa ci gaba musamman ta hanyar samar da zaman lafiya domin hakan ya zama darasi ga matasa da ma sauran yara kanana masu tasowa baki daya, sannan kuma ya shawarci al’ummar Hausawa mazauna unguwar Mile 12 da ma sauran unguwanni da ke cikin garin Legas da su zauna lafiya da sauran kabilu mazauna yankin su kuma hada kawunan junansu a wajan gudanar da harkokin rayuwarsu da sauran a’lamuransu na yau da kullum domin samun zaman lafiya mai dorewa a jihar da ma kasar baki daya.

A jawabin nasa, Dallatun ya jinjinama dattawan kasuwar ta Mile 12 da sauran shugabannin bangarorin kasuwar bisa jajircewarsu tare da bashi hadinkai da goyan baya, wanda a cewar sa, hakan ne ya sanya suke samun nasarorin gudanar da jagoranci mai kyau a kasuwar da kewayenta baki daya. Dattawan kasuwar dai solar hada da tsohon shugaban kasuwar Alhaji Isa Muhammad mai shinkafa kuma shugaban kungiyar amintattun dattawa na kasuwar, Alhaji Haruna Muhammad magayakin Jarman katsina wanda shima tsohon shugaban kasuwar ne, Alhaji Habu Faki Garkuwan Faki, Alhaji Abdulwahab Tsoho Babangida, Alhaji Abdullahi Burama da tsohon sakataren kasuwar Alhaji Wada yaro kiru da dai sauran su.
Ya cigaba da cewa, babu shakka wadannan bayin Allah sunayin iyakacin kokarin su wajaN ciyar da kasuwar gaba da alummar cikin kasuwar ma baki daya, sannan kuma ya ce yana mai matukar farin ciki tare da taya

Alhaji Haruna Muhammad Tamarke murnar samun nadashi wannan sarauta ta Magayakin Jarman Katsina, da fatan Allah ubangiji ya taya shi rikon al’umma baki daya, daga karshe ya ce yana mai kara farin cikin taya yan uwa musulmi murnar zagayowar watan azumin Ramadan na bana mai albarka da yan uwa musulmi suke gudanar da ibada a cikinsa da fatan Allah ubangiji ya sanya ibadar ta zamo karbabbiya ce yana mai rokawa, tare da fatan Allah ya cigaba da zaunar da kasar nan lafiya baki daya.

What's On Your Mind?