APC Ke Kitsa Kone-konen Ofisoshin INEC A Kasar Nan – jam’iyyar PDP

Jam’iyyar PDP ta zargi APC da alhakkin kone ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Jam’iyyar PDP ta bayyana ce, gwamnatin APC na kone-konen ne saboda wani makirci da take da shi a boye a shekarar 2023. Ba wannan ba ne karo na farko da jam’yyar PDP ta zargi gwamnatin jam’iyyar APC da laifin kona ofisoshin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da aka yi a Kudancin kasar nan. Babban jam’iyyar adawar ta yi zargin cewa, APC ce ke da alhakkin ta da hargitsi saboda tana aiki kan samar da wani yanayi na gaggawa don dakile zabuka masu zuwa ganin cewa ba za ta iya cin zabe a kasar nan ba.

Sakataran yada labaran na jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan wanda ya yi wannan zargin a wani taron manema labarai ya ce ya damu da shirun da APC ta yi, yayin kone-kone da lalata kayan aikin INEC.

Da yake amsa tambaya kan kona ofisoshin INEC ya ce, “yayin da muka kusanci zaben shekarar 2023, muna cikin damuwa a matsayinmu na jam’iyya adawa cewa, APC da ke jagorantar gwamnatin tarayya ta yi shiru duk da irin kone-kone da ake yi a ofisoshin INEC.
“Kuma muna da shakkun cewa jam’iyyar APC ta gaza wa ‘yan Nijeriya kuma fahimtar cewa ba za ta iya cin zabe a gaba ba ne ke da alhakkin wannan rudanin, saboda suna aiki kan samar da wani yanayi na gaggawa don dakile zabubbuka masu zuwa.

“Idan INEC ba ta da sauran kayan da za ta gudanar da zabe, ta yaya za a gudanar da zaben. Ta yaya za a tabbatar da dimokuradiyyarmu.

“Jam’iyyar PDP ta damu makuka da cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin APC ta yi shiru, alhali kuwa a kalla an kone ofisoshin INEC guda 20,” in ji shi.

A shekarar 2020, jam’iyyar PDP ta reshen jihar Imo ta yi irin wannan zargi biyo bayan konewar ofishin INEC na jihar a ranar Lahadi, 2 ga watan Fabrairun 2020. Ta zargi jam’iyyar APC da alhakin kone ofishin hukumar ta zabe mai zaman ta kasa, a cewarta saboda ta shirya ta sake yin duba ga hukuncin da ta yanke a kan zaben gwamnan Imo na 2019.

Comments (0)
Add Comment