Amfanin Reference Number wajen cika Neman Rancen Kudin Covid19 Loan

0
217

Amfanin Reference Number wajen cika Neman Rancen Kudin Covid19 Loan

Mutane sukan takura kansu da tambaya idan an cika musu wannan loan din wai ina reference number nasu, nakance musu bashi da wani amfani idan an gama cikawa yana aiki ne kawai a yayin da ake cikawa, kamar yanda suka fada.

To alhamdulillahi wannan sanarwa ta fito daga wajen masu bada wannan kudi.

Bidiyo : Tofah Limamai Sun Fara Aike Ma Gwamna Ganduje sako mai Zafi Akan Alert

Inda sunka wallafa a shafin suna cewa.

Amfanin reference number a lokacin da kake cika bayyananka/ki,tana da amfani ne a lokacin da kake cewa baka kamala ba, sai ka dawo mai makon ka fara daga farko zaka ga wajen an sanya ‘New’ ko ‘Returning’ to idan har kasan kana kusa kamalawa sai anka samu matsalar network ko data ka/ki ta kare a nan ne ake amfani da Reference Number domin komawa asalin inda kake domin kamala cika bayyanka sai ka zabi ‘returning’ zaka ga sun tambayeka ita,amma idan ka kamala cika bayananka shikenan babu wani amfaninta a gurinka/ki.

Allah yasa akace.

Amfanin Reference Number wajen cika Neman Rancen Kudin Covid19 Loan

What's On Your Mind?