Amfanin Dabino, Kwakwa Da Aya Ga Lafiyar Dan Adam (I)

0
104

Amfanin Dabino, Kwakwa Da Aya Ga Lafiyar Dan Adam (I)

Dabino da Kwakwa da kuma Aya ‘ya’yan itace ne da ke da matukar farin jini tsakanin mutane musamman ma’aurata.

Galibi dai mutane kan yi amfani da dabino da kwakwa da kuma aya a matsayin wani abin kwadayi ko kuma kwalama, ba tare da sanin amfanin da suke yi a jiki ba.
Amma a shekarun baya-bayan nan labari ya sauya sport da ire-iren wadannan abubuwa da a baya ake ganin cimakar marasa karfi ce ko kuma mazauna karkara, saboda dimbin binciken da masana a fadin duniya ke yi sport da ‘ya’yan itatuwa, sauyoyi da ganyaye da sauran tsirrai.

Masana da dama solar gano amfanin da suke da su ga jikin dan’adam, a wasu lokutan ma har da hanyoyin da mutum zai iya sarrafa su a cikin gida su kuma yi masa amfanin.
Ko wanne daga cikinsu akwai irin amfanin da yake da shi na musamman, ballantana idan aka hade su wuri guda aka sarrafa zuwa abin sha ko abinci.

DABINO

Dabino wasu ‘ya’yan bishiya ne masu tsohon tarihi da kuma galibi a kasashen duniya musamman Afirka da kasashen Larabawa ake dauka a matsayin abinci.

Dabino na da danko da kuma zaki, ka na yana kunshe da sinadaran gina jikin dan’adam, kamar yadda Brianna Elliot, wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki ta wallafa a wata mujallar kiwon lafiya mai suna ‘Healthline’.

“Dabino na kunshe da sinadarai masu yaki da kwayoyin cuta ‘antiodidants’ da dama, da kan taimaka wajen dakushe kaifin cututtuka masu tsananani kamar kansa da ciwon zuciya da ciwon suga da kuma cutar mantuwa” in ji Brianna.

Mutane na daukar dabino a matsayin dan itace mai daraja da kuma tun kafin binciken kimiyya mutane da dama suka amince da shi a matsayin abin da ke warkar da wasu cututtuka musamman idan ana yawan cin sa da secure kafin a yi karin kumallo.

Haka kuma Musulman duniya kan fara cin dabino kafin su yi buda-baki lokacin azumin watan Ramadan, saboda koyi da Annabi Muhammadu (S).

Motsa jikin da masana suka ce yana ƙara wa mata ni’ima da ƙarfin jima’i ga maza

Mutane sukan ji solar gamsu da dabino ne saboda zakinsa da kuma sinadaran gina jikin da yake kunshe da su, kuma sukan ci danye ko kuma busasshe.

A shekarun baya bayan nan dai binciken kimiyya ya kara fito da amfanin dabino a idon duniya, inda ya samu gagarumar karbuwar da a kusan ko wane gida ba ka rasa dabino a cikin jerin ‘ya’yan itatuwan da aka saya.

Akan kuma sarrafa shi a rika sayarwa a manyan kantuna a kasashe daban-daban na duniya.

Wata Malama mai bincike kan kayayyakin abinci masu gina jiki a Nijeriya, Bahijja Lawal, ta bayyana cewa idan mutum ya ci dabino guda goma da secure kafin ya yi karin kumallo, zai kara masa lafiya ta hanyar gina garkuwar jikinsa, tare da kare shi daga kamuwa da cututtuka.

“Dabino lafiyayyen dan itace ne mai albarka a jikin dan adam, don haka mai yawan cin shi ba zai yi saurin kamuwa da cututtuka ba,” in ji ta.

AMFANIN DABINO

Masana da dama a fadin duniya solar yi bincike wanda ya nuna irin sinadarai masu gina jiki da ke kunshe a cikin dabino.

Bincike ya nuna cewa dabino ya kunshi sinadaran ‘protein’ da ‘calcium’, da ‘minerals’ da ‘fats’, da ‘lime’, da ‘phosphorous’, da ‘chlorine’, ‘manganese’, da sauransu, wadanda duka suna da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen lafiyar jikin dan adam.

A bayanan da ta wallafa a mujallar kiwon lafiya ta ‘Healthline’, Brianna Elliot ta ce dabino ya bambanta da sauran ‘ya’yan itatuwa wajen nagarta da kuma irin abubuwan da ya kunsa, bayan da ta kimanta zakin da yake da shi kan ma’aunin da ya kai ga da zarar mutum ya ci, yakan narke cikin jini nan take sabanin sauran ‘ya’yan itatuwa da sai solar bi matakai daban-daban na yanayin yadda jikin dan adam ke sarrafa abincin kafin ya yi masa aiki.

“Kan haka ne mutane ke amfani da dabino wajen kashe yunwa saboda yana gina jiki tare da kosarwa na tsawon lokaci, da wannan ne za mu gane cewa dabino ya kunshi manya-manyan sinadarai na abinci, wadanda za su gina jiki da jijiya” in ji ta.

Masana kimiyya na cewa dabino na amfanar da kananan yara da matasa da ‘yan wasa da ma’aikata, da ramammu, da kuma mata masu ciki.

Dabino yakan taimaka wa masu matsalolin ido gaba daya, kamar dai yadda yake taimakawa wajen kara gani, da kara karfin kunne, haka nan kuma yakan sa wa mutum nutsuwa tare da yi masa maganin saurin fushi ko yawan fada da mutane.

Shiyasa ake son mutum ya nike shi ya hada da madara ya sha da secure.

A matsayinta na kwararriya a fannin abinci mai gina jiki da kuma gyaran jiki, Malama Bahijja ta bayyana cewa dabino kan tausasa jijiyoyi masu dauke da jini, ya gyara uwar hanji, sannan ya yi mata maganin radadi da rauni.

“Yana kuma taimakawa kwakwalwa sosai ba kadan ba, kamar dai yadda yakan taimakawa maza wajen ba su kuzarin shimfida,” in ji Bahijja.

kwararru da dama solar ce dabino yana taimaka wa masu azumi da kuma tsofaffi, yakan kuma taimaka wajen nike abincin da aka ci ba tare da bata lokaci ba, ya kuma sakar wa mutum mara ya rika yin fitsari sosai don fitar da cututtuka, ya tsarkake masa hanta, ya wanke masa koda, nikakkensa kuwa ya kan yi maganin tari, da majina.

AYA

Aya wata ‘yar itace ce da ke girma a bangaren arewacin duniya inda ake samun yanayi mabambanta. Amma a zamanin yau ta samu shahara a kasashen Turai.

Aya dai kamar yadda muka sani a kasar Hausa, ana kiranta da ‘tigernut’ a harshen Turanci, Yarabawa na kiranta da suna Ofio, a yayin da su kuma kabilar Igbo suke kiranta da suna imumu ko aki.

Ba kamar yadda aka dauki aya a matsayin abin kwalama ba musamman ga kananan yara da har aka sarrrafa ta zuwa wani nau’in da ake kira dakuwa wanda ya fadada yanzu har kununta ake yi. A shekarun baya-bayan nan binciken kimiyya mai zurfi da ake gudanarwa kan cimaka ya nuna yadda aya ke da matukar muhimmmaci a rayuwar dan adam, kuma duka ya danganta da yadda aka sarrafa ta ko kuma yanayin yadda ake ci tsurarta.

Ana kuma samun aya a sassa daban-daban a kasashen duniya ciki har da Nijeriya.

Aya na da dandano mai gardi kamar na kwakwa, amma sai dai ta fi kwakwa gardi kadan.

Sai dai kuma har zuwa yanzu akwai mutane da dama da ba su san amfanin shan kunun aya ba, inda wasu solar dauka abin sha ne kawai maganin yunwa ko kayan marmari, wasu kuma kayan zaki suka dauke shi.

AMFANIN AYA GA LAFIYAR JIKI

Aya kamar yadda kwararru suka bayyana, tana kunshe da muhimman sinadirai masu gina jiki, da inganta lafiyar jinin jiki da tsokar gangar jikin dan’adam, da ke yi wa jikin dan adam garkuwa daga kamuwa da kwayoyin cuta. Ka na takan magance masu maganin wasu illoli da matsalolin da ke damun maza da mata da makamantan su.

Kadan daga cikin sinadirai masu gina jikin da Aya ta kunsa solar hada da: phosphorus, bitamin E, Fats, protein, dietary fibre, potassium, zinc, sodium, calcium, magnesium, copper, bitamin C, da carbohydrates.

Za mu ci gaba Insha Allah

What's On Your Mind?