Kaddamar Da Aikin Hanya: Al’ummar Garin Danguguwa Sun Ce Suna Tare Da Jobe

0
128

Al’ummar Garin Danguguwa Sun Ce Suna Tare Da Jobe

Wakilin al’ummar Rimin gado da Dawakin Tofa da Tofa a majalisar tarayya Hon. Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe ya kaddamar da aikin yin hanyar Kwanar Kwakwacu zuwa Danguguwa.

Da yake kaddamar da aikin hanyar a madadin dan majalisar tarayyar. Wanda ya wakilce Dakta Kamilu Dawakin Tofa ya ce, aikin da dan majalisar yake na da alaka da damarda suka bashi na zabarsa da suka yi.

Ya ce, Dan majalisar na tarayya ya ce, a bayyanawa al’ummar yankin cewa shima dan danguguwa ne kuma ayyuka da dama an kawo su garin akwai Asibiti da samar da ruwa da gyaran wutar lantarki da  tallafi da taimako da ake.

Kwalejin Koyon Aikin Jinya Da Ugozuma Ta Yaye Dalibai 63 A Kebbi

Ya ce, yanzu Allah ya kawo lokaci da ake kaddamar da wannan aiki daga Kwanar kwakwaci zuwa Danguguwa suna godiya ga Allah da yabo ga Gwamna da shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa da dan majalisar jaha da fatan Allah ya sakawa Injiniya Jobe da alkhairi.

Dokta Kamilu ya ce, wannan aikin na raya kasa da dan majalisar tarayya yake kari ne akan  ayyukan gina makarantu da asibitoci da al’ummar Danguguwa za su zama shaida akai.

Anasa jawabin daya daga al’ummar yankin na danguguwa. Alhaji Faruk Danguguwa ya ce, photo voltaic tabbatar da cika alkawarin dan majalisar mutum ne mai rike alkawari.

Ya ce, tun a baya hanyar bata daga cikin wanda za a yi amma ya yi alkawarin sata a ciki kuma hakan ta tabbata an zo za a yi. Kuma ya ce, mutanen garin danguguwa mutane ne masu biyayya masu bada hadin kai ga Injiniya Jobe a koyaushe.

What's On Your Mind?