Al’umma A Ci Gaba Da Addu’oin Kawo Karshen Rashin Tsaro – Shugaban Majalisar Kaduna 

- Advertisement -

Al’umma A Ci Gaba Da Addu’oin Kawo Karshen Rashin Tsaro – Shugaban Majalisar Kaduna 

Daga Abubakar Abba,

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Rt. Honarabul

Yusuf Ibrahim Zailani, ya bukaci daukacin al’ummar Musumai da ke a kasar nan ka da su gajiya wajen yin addu’oi domin Allah ya tsamo kasar daga cikin lamarin rashin tsaro da ya addabe ta.

“Ina kira ga daukacin al’ummar Musulmai a kasar nan ka da su yi kasa a gwiwa wajen yin addu’oin Allah ya kawo mana karashen sace mutane da kuma ta’addanci da ya addabi kasar nan.”

Zailani wanda kuma shi ne shugaban kungiyar shugabannin Majalisun Dokikin Arewacin kasar nan ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da hadiminsa na yada labarai Ibrahim dahiru danfulani ya raba wa manema labarai a Kaduna.

Shugaban a sakonsa ga Musulman na karamar Sallah ya kuma ta ya daukacin al’ummar Musulmi da ke a fadin jihar, na Arewacin kasar da kuma na fadin duniya bisa kammala Azumin watan Ramadan lafiya da kuma gudanar da shagulgulan na karamara Sallar.

A cewar Zailani, “Ya kamata mu Musulami mu yi amfani da darusan da muka koya a yayin gudanar da Azmin wajen yi wa kasar mu addu’ar Allah ya kawo mana karshen matsalar rashin tsaron da take ciki”

Zailani ya kuma shawarci ‘yan Nijeriya da su kawar da banbancin kabila ko na addini domin ci gaba da zamo wa ‘yan uwan juna.

- Advertisement -