Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi Sun Yi Sallar Idi A Yau

- Advertisement -

Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi Sun Yi Sallar Idi A Yau

Daga Khalid Idris Doya

A yau Laraba ne ‘yan Darikar Tijjaniyya suka gabatar da Sallar Idil Fitr a Bauchi, inda dubban jama’a suka hallara a gidan Shaikh Dahiru Usman Bauchi domin gabatar da wannan sallar Idi mai raka’a biyu.

An yi Khudubar Idi da kuma sauran jabawan da suka gabata, inda babban Dan Shehin, Ahmad Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi ya jagoranci Sallar bisa umurnin Sheikh Dahirun.

A cikin Khudumarsa ya jawo hankalin jama’a dangane da jin tsoron Allah cikin lamura tare da yin addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar nan.

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida bayan gabatar da Sallar Idin, Babban Malamin Darikar Tijjaniya a Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewar solar ajiye Azumin watan Ramadana ne bayan da suka tabbatar da ganin watan Shawwal daga adilan mutane.

Ya kuma bayyana cewar batun Azumin watan Ramadana yana nan a cikin addini bisa koyarwar Manzon Allah (S) don haka suke bin umarnin Annabi, “Duk abun da ka ga ana yi a addini Annabi ne ya karba wa mutane, idan Annabi yayi magana to maganar kowa ta kare, maganarsa kawai ake ji, ba a jin maganar kowa daga maganar Allah sai maganar Annabi da yake mana tarjama. To Annabi ya ce, “Idan kun ga watan Ramadana ku kama Azumi, idan kuma kuka ga watan Shawwal ku ajiye azumi, idan kuma watan Azumi ya kare ba ku ga wata ba sai ku cika Azumi zuwa 30, idan kuma wata bai buya ba an ganshi mene ne uzuri?.

“Kuma bamu da ikon mu karyata wadanda suka ce solar ga wata din nan. akwai wadanda solar a watan Shawwal a Bauchi, ni dai kaina ma na ga mutumin da ya gani, a Gombe, an gani a Gadau, an gani a Argungu, da sauran garuruwa ba za mu karyata duk wadanda nan kawai mu ci gaba da Azumi a watan Shawwal.”

Ya ce su da suke da hujjarsu na yin Sallah a ranar Laraba wadanda basu yi sallar ba suma suna da nasu hujjar na daban, “Mu abun da ya sanya muka yi sallah a yau muna da hujjarmu, su ma abun da ya sanya basu yi sallah ba suka ci gaba da Azumi suna da hujjarsu wanda ba mu san wacce iri ce ba.”

Ya kuma bayyana cewar dukkanin matakan da suka dace wajen ganin solar sanar da Sarkin Musulmi Sa’advert Abubakar dangane da cewa an ga watan Shauwal a ranar Talata solar bi, “Na buga waya na samu Sarkin Malaman Sokoto na ce ka-ji-ka-ji amma ka san yadda za ka isar wa Sarkin Musulmi, ya tabbatar min da cewa Insha Allahu zai isar, sannan kuma akwai wani masoyinsa, abokin aikinsa Sarkin Kafin Argungu shi ma na buga masa cewa ga shi mutane solar kawo min labarin solar ga wata wanda ni na yarda da shi, a kuma fada wa Sarkin Musulmi an ga wata. Shi ma ina tsammani zai gafa masa.”

Har-ila-yau, ya kuma bayyana cewar matakan da suka dace duk su isar wa Sarkin Bauchi shi ma solar bi domin ganin solar isar da saqonsu ga waxanda suka dace.
Dangane da rikita-rikitan ganin wata da ake samu a shekaru da dama a Nijeriya, Shehin ya bayyana cewar mafitar guda ita ce a bi abun da Allah ya ce, “Matakai kawai sai bin maganar Annabi (S) a bi maganar Annabi kawai da yake cewa, ‘In kun ga wata ku kama Azumi, In kun ga wata ku ajiye Azumi. to an riga an ganshi ya aka iya? Mafitar a koma ga maganar Annabi.”

Kan masu kokarin daidaita ganin watan Nijeriya da na kasar Saudiyya kuwa, Shehi Dahiru ya bayyana cewar akwai rashin sanin addini cikin lamarinsu, “Wannan ai jahilci ne yanzu lokacin da Saudiyya suka yi Sallar protected nan mu za mu yi? Ai dare ne lokacin, lokacin da Saudiyya suka yi sallar Azahar za mu yi? Ai lokaci bai yi ba hantsi ne a wajenmu, lokacin da suka yi La’asar za mu yi? Lokacinmu bai yi ba don kusan Azahar ne a nan, lokacin da za su yi Magriba rana ta fadi a wajensu mu kuma muna ganin rana kwal sai mu yi sallar magriba don saudiyya ta yi?” ya taimabaya.

Dangane da matsalar tsaro, babban malamin ya yi addu’ar Allah zaunar da kasar nan lafiya tare da kira ga hukumomi da su kara azama wajen kare rayuka da dukiyar jama’a, yana mai cewa matsalar tsaro na masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga gami da ‘yan Boko Haram matsaloli ne da suke neman wuce gona da iri wanda ya nemi hukumomi su qara kokari domin kawo karshen hakan.

Za mu buga cikakken labarin yadda sallar ya gudana a fitowar jaridarmu na gobe

- Advertisement -