Allurar Rigakafin Cutar COVID-19 Ta Kamfanin Sinopharm Na Kasar Sin Ta Samu Izinin WHO

- Advertisement -

Allurar Rigakafin Cutar COVID-19 Ta Kamfanin Sinopharm Na Kasar Sin Ta Samu Izinin WHO

Daga CRI Hausa

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar a jiya Juma’a cewa, allurar rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin, ta samu izinin hukumar na amfani da ita a matakin gaggawa, hakan ya sa allurar Sinopharm ta zama irinta ta 6 da ta samu izinin WHO, kuma allura daya tilo ta kasar da ba ta yammacin duniya ba.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana yayin wani taron manema labarai cewa, wannan mataki zai taimaka wajen habaka allurar da shirin COVAX zai saya a duniya, kuma zai karfafa gwiwar kasashen duniya wajen gaggauta amincewa da allurar don amfani da ita a kasashensu. (Amina Xu)

 

- Advertisement -