Allah yayiwa Mahaifin Jaruma Maryam Gidado Rasuwa

0
296

NNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa mahaifin fitacciyar jarumar finafinan Hausa Maryam Jibrin Giɗaɗo rasuwa.

Alhaji Jibrin Giɗaɗo ya rasu ne jiya a Bauchi bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Mujallar Fim ba ta samu cikakken bayani kan rasuwar ba, amma ta samu labarin cewa marigayin ya rasu ya bar matar sa da ‘ya’ya.

Maryam Malika Ta bayyana Matsayin Aurenta a Yayin cike Form din zama cikakkiyar Jaruma a Kannywood

Daga cikin ‘ya’yan nasa har da ita Maryam Giɗaɗo wadda ake wa laƙabi da ‘Maryam Babbanyaro’ da kuma ƙanwar ta Hon. Hajara Jibrin Giɗaɗo wadda ita ce Kwamishinar Harkokin Mata Da Inganta Rayuwar Ƙananan Yara ta Jihar Bauchi.

An riga an yi jana’izar mamacin kamar yadda Musulunci ya tanadar.

Allah ya jiƙan Alhaji Jibrin Giɗaɗo, ya ba iyalan sa haƙurin jure wannan babban rashi, amin.

What's On Your Mind?