Ali Nuhu Yayi Martani Akan Zarge Zargen Da Ake musu Akan Haukacewar Ashiru Nagoma

0
29

A cikin wata tattaunawa da shafin dokin karfe sunkayi da ali nuhu akan haukacewar shahararen mai bada umurnin masana’antar Kannywood.

Ga yadda tattaunawar ta kasan ce

Tantabarun da Buhari ya saki a bikin ranar tunawa da Sojoji sun ki tashi

“A cikin tattaunawar da mu ka yi da Ali Nuhu, ya musanta zarge-zargen da ake yi musu na watsi da Ashiru Na Goma bayan ya gamu da rashin lafiya. “Tsawon shekaru da su ka wuce, mun yi ƙoƙarin kai Ashiru Na Goma Asibitin da za a riƙa kula da shi har zuwa lokacin da Allah zai ba shi lafiya amma mahaifiyarsa ta ce sam ba ta yarda ba, ɗanta lafiyarsa ƙalau babu wanda zai kai mata shi asibiti”. Cewar Ali Nuhu.

Ali Nuhu Yayi Martani Akan Zarge Zargen Da Ake musu Akan Haukacewar Ashiru Nagoma

Ali Nuhu ya kuma ƙara da cewa bayan rasuwar mahaifiyar Ashiru Na Goman solar cigaba da wancan yunƙuri na kai shi asibitin amma nan ma ƴan uwansa su ka hana. “Ƴan uwan Ashiru Na Goma su ma solar ce ba su yarda mu kai shi asibiti ba bayan rasuwar mahaifiyarsa, amma tunda su ne ahalinsa na jini babu yadda mu ka iya ala dole mu ka haƙura da kai shi asibitin nema masa magani, amma duk da hakan ba mu ƙyale shi kara zube ba, mu na tallafa masa domin ni har gidana ya na zuwa ina kuma kyautata masa”. Inji Ali Nuhu”

 

What's On Your Mind?