Alhaji Abdussalam Zaura Ya Karbi Katinsa Na APC

0
81

Alhaji Abdussalam Zaura Ya Karbi Katinsa Na APC

Daga Ibrahim Muhammad,

Tsohon dan takarar Gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar GPN, Wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura ya ziyarci mazabarsa ta Rangaza dake Zaura Babba inda ya karbi katin zama cikakken dan jam’iiyyar a ranar Asabar.

 

Dafifin magoya baya da jagororin jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Ungogo da suka hada da shugaban Karamar Hukumar, Injiniya Dokta Abdullahi Garba Ramat da Dan majalisar tarayya mai wakiltar Ungogo da Minjibir, Hon. Sani Ma’aruf Mai wake da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar ne suka shaidi karbar katin.

 

Mataimakin shugaban riko na jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Shehu Meigari ne ya jagoranci mika wa Alhaji A.A. Zaura katin zama dan jam’iyyar na APC.

 

A jawabinsa ga dandazon jama’ar da suka taru a akwatinsa na mazabar Tangaza a Zaura Babba, Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura ya bayyana mutukar farin ciki da jin dadinsa bisa wannan rana mai muhmamci da ya karbi katin shaida na shigarsu da magoyansa Jam’iyyar APC mai albarka a cikin wata mai alfarma na Ramadan.

 

Ya ce ya shigo ya sami mutane da suke tafiya tamkar uwa daya uba daya kuma su da suka shigo za su yi zamam tare na gaskiya da amana a tsakaninsu ta yadda za a gina jam’iyyar za su zama tsintsiya daya madauri daya.

 

Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura yace  dukkan magoya bayansa  na GPN daga kananan hukumomi 44 su zo su yanki katin APC tun daga kan mazaba har jaha solar koma APC.

 

Shi ma a nasa  jawabin shugaban karamar hukumar Ungogo, Injiniya Dokta Abdullahi Garba Ramat ya ce suna yi wa Allah godiya domin ita siyasa kamar daki ce mutum daya ba ya iya yin siyasa sai an samu mutane da yawa kuma yawanku da karfinku a siyasa.

 

Yau ace a jam’iyyar  APC manyan mutane da suka yi takarar Gwamna solar shigo cikin jam’iyya wannan ba karamin abin alfahari bane. Wannnan abin alkhairi ne da yake samuwa sakamakon aiki da mai girma Gwamnan jahar Kano yake, shi ya sa ake sha’awar shigowa jam’iyyar.

 

Ya ce su a APC duk wanda ya shigo sabo basa nuna bambamci, shi ma asali daga wata jam’iyya ya shigo APC gaba daya bai fi shekara Biyu a ciki ba ya zama manajan darakta yanzu kuma shi ne zababben shugaban karamar hukumar Ungogo wanda wannan shaidane akan kaina na cewa duk wanda ya shigo sabo za’a mutuntashi a bashi daraja sosai.

 

Hon. Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya ce a matsayinsu na shugabanni kuma musulmi irin abubuwa suke ba wai damakwaradiyya bace kadai hakkine akan duk wani musulmi dake shugabantar jama’arsa ya bisu duk inda suke sako da lungunsu yayi musu hidima.

What's On Your Mind?