Akwai Rufin Asiri A Sana’ar Haya Da Babur– Ciyaman Suleman Salisu Legas

0
82

Akwai Rufin Asiri A Sana’ar Haya Da Babur– Ciyaman Suleman Salisu Legas

Wani Shugaban kungiyar masu sana’ar haya da babura a legas wadda akafi sani da suna sana,ar okada atakaice mai suna suleman salisu wanda ya ke zaune a kan titin Uwutu Ishawu street da ke agrick ta karamar hukumar Ikorodu a cikin garin Legas, ya bayyana cewar akwai rufin asiri matuka tare da da samun nasarar mallakar abin dogaro da kai a cikin sana’ar su ta masu haya da babura a Legas da kewayenta.

Shugaban kungiyar ta masu sana’ar Okada a Uwutu Ishawu a unguwar Agrick ya yi wannan bayani ne aofis din kungiyar jim kadan bayan kammala taron su da sauran mambobin wanda suka saba yi a kowanne karshen wata domin tattaunawa a bisa kan abubuwan da za su cigaba da kawo cigàban kungiyar da kuma dakile faruwar a kasin hakan.

Majalisar Dokokin Bauchi Ta Gargadi ’Yan Kwangila Bisa Aikata Ha’inci

Bayan kammala taron nasu ne sai na kebe shugaban domin jin tabakinsa recreation da ayyukan da kungiyar tasu ta gabatar da kuma wadanda take shirin yi anan gaba inda shugahan kungiyar Suleman Salisu ya kada baki yana mai cewar babu shakka daman ita wannan kungiyar tasu solar kafata domin su taimaki kansu da kansu, ya kuma ce, Alhamdulillahi solar samu nasarori masu yawa agame da kafa ita wannan kungiyar ya ce na farko dai solar kaddamar da yuniyon wadda za ta cigaba da kulawa da zirga-zirgar mambobin kungiyar a lokacin da suke haya da baburan su tare da kare masu hakkokin su na yau da kullum sannan kuma ya ce, suna yi wa mambobin kungiyar kokari musamman wadanda ya kasance basu da mashin a hannun su indai baya yin wasa da balas yana cika alkawari a kowanne lokaci kungiya za ta yi iyakacin kokarinta a wajen ganin ka samu mashin domin ganin ka cigaba da neman abincin ka.

Ya kuma ce, ya mai bayar da shawara ga matasan kasar nan dasu rage fadin rai su ajiye komai dake cikin zuciyar su na cewar na yi karatun boko aikin gwamnati kawai nike jira dasu ajiye wannan waje guda su rungumi wannan sana’ar ta haya da babur wadda akafi sani da suna okada.

What's On Your Mind?