Akwai Lauje Cikin Dadi, Alakar Dake Tsakanin Maryam Da Sani Danja

- Advertisement -

Maryam Abubakar Sharif wacce aka fi sani da Maryam Jan Kunne ta bayyana cewa a can baya Sani Danja ya sota kuma tayi fina-finai a ma’aikatar shi, amma a yanzu kuwa babu wata alaƙa tsakaninta da jarumin sai dai mutunci kawai.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da maganar mutuwar auren jarumi Sani Danja da Mansurah Isah.

Maryam jan kunne tayi wannan bayani ne a cikin wata hira da gidan rediyon BBC Hausa cikin fitaccen shirin na nasu na daga bakin mai ita. Ta ƙara da cewa laƙabin da ake mata na Maryam Jan kunne ya samo asali ne daga wani shiri na faɗakarwa mai suna ‘Jan kunne’ da ta fito a ciki.

Jarumar dai tayi tashe a harkan film ne daga shekarar 2005 data fara zuwa shekarar 2008 data bar masana’antar bisa dalilin aure data yi. AlLah ya albarkaci auren nata da ƴa ƴa guda biyu; mace da namiji. Sai dai jaruma maryam jan kunne ta bayyana cewa a yanzu bata da aure saboda wancan auren da tayi ya mutu.

Maryan jan kunne da ya yanta:-

Da aka tambaye ta kan ko tana da sha’awar komawa film? Jarumar ta bayyana cewa zata iya komawa amma ba akan kowanne film ba, sai wanda taji labarin mai ma’ana ne kuma zai faɗakar sannan ya amfanar da mutane.

Ta ƙara da cewa akwai wasu ƴan harkoki data keyi wanda a dalilin haka ba zata iya dawowa masana’antar Kannywood ta tare din-din-din ba. Sai dai ta bayyana cewa zata riƙa fitowa jefi-jefi a fina-finan da taga zasu bada ma’ana.

Ta bayyana sunan film din da zata fara bayyana a cikinsa da sunan ‘Jan Kunne’ wanda shima zai zamto akan faɗakarwa ne kamar yadda akayi wancan na jan kunnen na baya.

Da take amsa tambaya kan yadda ake zagin ƴan film, Maryan jan kunne ta bayyana cewa duk da dai ɗan kuka shine ke janyo ma uwarshi jifa, sannan kuma kowa abinda ya aikata dashi ubangiji zai yi mishi hukunci.

Daga ƙarshe tace burinta shine ta gama film lafiya (in AlLah yasa ta koma ɗin), tayi aure sannan ta cika da imani.

- Advertisement -