Aikin Noma Na APPEALS  Ya Bunkas Sana’ar A Legas In ji Manoma

0
64

Aikin Noma Na APPEALS  Ya Bunkas Sana’ar A Legas In ji Manoma

Daga Abubakar Abba

 

Fannin aikin noma ako wacce kasa na taimaka wa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar domin babu kasar da  za ta iya ci gaba idan ba ta yin noma,  inda hakan ya nuna cewar,  wajibi ne a samar da wadataccen abinci.

Hakan ne ya kasance daya daga cikin dililan da ya sa Gwamnatin Tarayya da kuma gwamabtocin jihohi  dake kasar nan  suke taka muhummiyar tawa wajen kara bunkasa aikin noma.

Daya daga cikin manyan shirye-shiyen  aikin noma da gwamnatocin suka mayar da hankali wajen bunkasa aikin noman shi ne,   aikin noman na   (APPEALS).

Aikin noman na  APPEALS, an tsara shi kan shekaru shida wanda kuma ake sa ran za a gudanar dashi daga shekarar  2017 zuwa shekarar  2023.

Aikin dai Bankin Duniya ne yake bayar taimako wajen wanzar dashi ta hanyar ma’aikatar aikin gona da raya karkara a jihohi shida da suka shiga cikin shirin.

Jihohin da suka shiga cikin aikin solar hada da,    Koros Riba,  Enugu, Kaduna, Kano, Kogi da kuma Legas kuma aikin na kan daiai da tsarin habaka noma na   (APP) da Gwambatin Tarayya ta faro daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2020.

Har ila yau,  aikin an kafa shi ne  bisa manufar ajandar habaka fannin aikin noma   na  (ATA) da kuma shirin samar da wadataccen abinci,  samar da ayyukan yi da kuma habaka tattalin arziki kasar nan.

Bugu da kari,  daga cikin jihohin shNo da da suka shiga cikin sirin a kasar nan,  jihar Legas a yi namjin kokari a aikin na  APPEALS,  musamman wajen cimma burin manufar aikin dake da kudurinkara bunkasa matsakaitan da mabyan sana’oi da ka kara habaka fannin kiwon Kaji da noman Shinkafa.

Har ila yau,  tun lokacin da aia fara wanzar da aikin na APPEALS a jihar Legas,  Jami’ar aikin ta jihar Legas   Uwargida  Oluranti Sagoe-Obiebo tare da kuma tawagarta,  solar mayar da hankali wajen habaka kanana da matsakaitan sana’oi a jihar.

A yau,  aikin na APPEALS a  jihar Legas,  ana samu cin nasara musamman ganin yadda aikin ya kara bunkasa fannin aikin noman jihar da kuma inganta rayuwar dubban manoman dake a jihar.

Bugu da kari,  wadanda suka amfana da aikin  na APPEALS solar bayyana cewa,  solar amfana fa aikin matuka.

Za a daga cikin ya’yan kungiyar aikin noma ta Isokan   dake a yankin Agbowa-Ikosi a cikin karamar hukumar  Ikosi-Ejirin  Mista  Ademola Subair ya bayyana cewa, aikin na   APPEALS ma jihar Legas ya samar masu da sauki matuka.

What's On Your Mind?