Ahmed Bamalli Ya Zama Sarkin Zazzau

0
84

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da nadin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

Bamalli shi ne sarki na farko da ya fito daga gidan Sarautar Mallawa a cikin shekaru 100 da su ka gabata bayan kakansa, Sarki Dan Sidi, wanda ya mutu a shekarar 1920.

Wata sanarwa wacce Kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu na jihar, Alhaji Ja’afaru Ibrahim Sani, ya fitar tana cewa, Bamalli ya gaji Alhaji Dakta Shehu Idris, wanda ya mutu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2020, a bayan da ya shafe shekaru 45 a kan karagar mulki.

Ahmed Bamalli Ya Zama Sarkin Zazzau

Sanarwar ta bayyana cewa: “Gwamna El-Rufai, ya taya sabon Sarkin, Mai Martaba Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, Murna a bisa nadin da aka yi masa, sannan ya yi masa fatan samun nasara da jan ragamar masarautar ta Zazzau a cikin kwanciyar hankali.

“Har ya zuwa lokacin nadin na shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya riki mukamin Sarautar Magajin Garin Zazzau, sannan ya yi aiki a matsayin jakadan Nijeriya a kasar Thailand, da kasar Myanmar.

Ya taba rike mukamin Kwamishinan dindindin a hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kaduna a shekarar 2015.

A cewar Kwamishinan kananan hukumomin, sabon Sarkin na Zazzau, ya yi aiki a banki a matsayin babban darakta, daga baya kuma ya zama mukaddashin babban darakta a kamfanin yin kudi na Nijeriya.

Hadiza Gabon na murnar zagayowar ranar haihuwar ‘yarta mai shekaru 7 da haihuwa

Ya kuma yi aiki a ma’aikatar hukumar babban binin tarayya kafin ya zama shugaban sashen ayyuka na kamfanin sadarwa na MTel, wanda wani sashe na tsohon kamfanin sadarwa ta kasa watau NITEL.

Bamalli wanda aka haife shi a shekarar 1966, ya karanci aikin lauya ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, yana kuma da digiri na biyu a kan harkokin dangantaka a tsakanin kasa da kasa, yana kuma da Diploma a kan harkar shugabanci wanda ya samu daga jami’ar Odford ta kasar Ingila, in ji sanarwar, ta kara da cewa, yana kuma da takardar shaida a kan hanyoyin sasanta rikici wacce ya samu daga jami’ar Unibersity of York, ita ma daga kasar ta Ingila (UK).

A nan gaba kadan ne kuma za a bayar da sanarwar lokacin nadi da kuma mika masa sandar sarauta, in ji sanarwar.

What's On Your Mind?