Adenike Osofisan: Mace Ta Farko Farfesar Kimiyyar Kwamfuta A Nahiyar Afrika

0
74

Adenike Osofisan: Mace Ta Farko Farfesar Kimiyyar Kwamfuta A Nahiyar Afrika

Ko-kun-san….

Adenike Osofisan itace macen da ta fara zama Farfesa ta farko a fannin kimiyyar sarrafa na’ura mai kwakwalwa a duk fadin Afrika?

A yau filin na dauke da tarihin wata jaruma, shahararriyar shehin ilimin sanin na’ura mai kwakwalwa wacce ta samu zarran kafa tarihi a duk nahiyar Afrika, da ta fara zama mace ta farko farfesa a darasin kimiyyar kwamfuta, malamar kwalejin kimiyya kuma malamar jami’a, ta yi fice a fannin ilimi sosai.

Wacece Adenike Osofisan?

An haifi Adenike Osofisan a ranar 11 ga watan Maris na 1950 Farfesar kimiyyar na’ura mai kwakwalwace (Laptop Science) wacce ta gwanance ta kware a fannin tattara bayanai da kuma kula da ilimi. Ita ce mace ta farko ‘yar Nijeriya da ta fara samun ilimi mai zurfi har zuwa matakin digirin digirgir (PhD) a fannin kimiyyar kwamfuta, wacce ta fara taka wannan damar tun a 1989. A shekarar 2006, ta zama cikakkiyar Farfesa a jami’ar Ibadan, hakan ya kai ta ga zama mace ta farko a dukkanin nahiyar Afrika da ta fara zama Farfesar kimiyyar kwamfuta.

Adenike Osofisan ta kammala karatun sakandarinta ne a Fiwasaiye Women’ Grammar College, da ke Akure, da kuma Comprehensice Excessive College, Ayetoro a 1968. A tsakanin 1971 da 1976, ta samu digirinta na farko a jami’ar Ile-Ife, ta samu tallafin karatu daga gwamnatin tarayya tun a wancan lokacin bisa kokarinta inda ta kammala jami’a cikin cin moriyar wannan tallafin. Daga baya ta zo ta wuce zuwa cibiyar ilmin kimiyya ta Georgia a 1978, ta samu digirinta na biyu ne a Info and Laptop Science a shekarar 1979. Ta kuma yi digirinta na uku (PhD) kan darasin ‘Information Processing Mannequin for a Multi-access Laptop Communication Community’ wacce ta kammala a 1989 a jami’ar Obafemi Awolowo a karkashin sanya idon Adebayo Akinde. A 1993, ne ta kammala wani shiri na musamman a fannin iya gudanar da harkokin kasuwanci da ririta kudade a jami’ar Ibadan.

Ayyukanta:

Farfesa Osifisan ta fara aikin koyarwa ne a kwalejin kimiyya ta Ibadan a shekarar 1979. Ta kwashe tsawon shekaru tana koyarwa a wannan kwalejin daga baya har ta zo ta zama shugabar tsangayar kimiyya na wannan kwalejin. A 1999 ne kuma ta fara aiki da jami’ar Ibadan, nan take ta fara aiki a matsayin mai rikon mukamin shugaban sashin kimiyya na jami’ar. A 2003, ta samu likafarta ya daukaka zuwa karamar farfesa, kama-kama ta samu zuwa ga matakin cikakkiyar Farfesa ne a shekarar 2006. Har-ila-yau, ta kasance malamar jami’ar da ke koyarwa na wucin gadi a jami’ar Legas.

Kungiyoyin da ta ke ciki:

Adenike Osofisan ta kasance mambar majalisar amintattu na Nigeria Web Registration Affiliation (NIRA); tsohowar mambar cibiyar ilimin lissafi ta kasa ‘Nigeria Mathematical Centre’ da Nigeria Institute of Administration (NIM) Councils.

Yanzu haka ita mambar majalisar ilimi ce; mambar Africa Tutorial Board of SAP (Techniques, Functions, and Merchandise in Information Processing).

Sannan kuma, Adenike ita ce Darakta a makarantar nazarin ilimin kasuwanci ta ‘Ibadan College of Enterprise’ (UISB). Ita ce mace ta farko da aka fara zama shugabar Nigeria Laptop Society School of Fellows a watan Yulin 2017.

Ta amshi lambobin yabo da na shaida da dama a rayuwarta. Ta kuma yi wallafe-wallafe na littafai da mukalolin da a yanzu haka ake amfani da su a cibiyoyin ilimi da daman gaske.

 

What's On Your Mind?