Adam A Zango Ne Mai Gidana – kuma Zan Iya Aktin Ko wanne irine, Horo Dan mama

- Advertisement -

Fitacen Jarumin Kannywood “MUHAMMAD Nasiru”, wanda ake wa laƙabi da Horo Ɗanmama, fitaccen jarumin barkwanci ne kuma mawaƙi a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood. Duk da yake ya daɗe da bautuwa a harkar, za a iya cewa ya na cikin ‘yan tsaka-tsaki wajen yin fice, wato ba kowa da kowa ba ne ya san shi.

To amma ya na aiki tuƙuru don tauraruwar sa ta ƙara haske.Shin menene tarihin sa? Da gaske ne ya taɓa zama yaron marigayi Ibro? A yanzu kuma mecece alaƙar sa da Adam A. Zango? Duk waɗannan tambayoyi Nasiru ya amsa su a cikin hirar sa da mujallar Fim, har ya ƙara da cewa ya na da wata baiwa wadda har zuwa yanzu jama’a ba su waye da ita ba. Shin wace baiwa ce wannan? Ku karanta wannan tattaunawar ku ji:

FIM: Za mu so ka faɗa mana tarihin ka a taƙaice.

NASIRU HORO: da fari, ni dai mutumin Gumel ne a Jihar Jigawa, amma mahaifi na ɗan garin Kano ne, mahaifiya ta kuma ‘yar Jihar Jigawa ce. To amma in ba sani na ka yi ba, duk wasu al’amura na na fiye yin su a Kano da kuma Kaduna, don tsakani na da Gumel sai dai in je mu gaisa da ‘yan’uwa na in dawo inda na ke.
Haka zalika ni jarumi ne a masana’antar Kannywood; a wani ɓangaren mawaƙi.

FIM: Ya aka yi aka tsinci kan ka a cikin wannan harka ta fim?

NASIRU HORO: To ni da man can mutum ne mai son nishaɗi, wanda haka kawai ma za ka ga ina ta waƙe-waƙe na. Kuma har yanzu wasu ba su san ina waƙa ba.

Ka san a lokacin da ka ke cikin wahalar waƙa amma akwai wani abu ɗaya da za ka yi in Allah ya yarda duniya ta sani sai ka ji an fara cewa, “Da man wannan yaron ya na waƙa?” To ba a san irin gwagwarmayar da ka sha a cikin wannan lamari ba. Duk da cewa wasu ba su gane mu ba, mun san Allah zai kawo yadda za a san cewa ni mawaƙi ne.

Harkar fim ɗin Hausa kuma gaskiya da man can ni mai ra’ayin ta ne tun a unguwar mu, don haka kawai za ka ga ina yin shiga haka ta ban-dariya, in shafa bula a fuska ta, har abin dai ya kawo wannan lokaci da mu ke ciki mu da mu ke kallo a da, amma yanzu kuwa mu ake kallo. Ba abin da za mu ce da Allah sai godiya.
Ta yadda na shiga Kannywood kuwa, da can asali na ina rawa. Na yi harkar rawar gidan gala, daga nan ma sai da na zo na zama lamba ɗaya a harkar rawa a lokacin. Sannan ba inda na ke zuwa sai gidan wasan marigayi Rabilu Musa Ibro; tun daga nan Kano na ke niƙar gari in tafi har zuwa garin Wudil in je in yi wasa na dawo. Sai da ya zamana a lokacin duk cikin yaran Ibro ba wanda jinin sa ya shaƙu da shi iri na. Kai, hatta waya ma in aka kira ta Ibro wani lokacin ni ya ke miƙa wa na ɗaga in yi musu irin muryar sa, kuma idan mutum bai sani ba ba ka isa ka ce ba Ibro ba ne ya yi maganar.

Sannan idan mai karatu zai iya tunawa, fim ɗi na da aka fara sa ni shi ne ‘Ibro Ɗan Foliyo’ wanda na fito a ɗan gidan Baban Chinedu a cikin fim ɗin, har Daushe ya zo ya na duka na Baban Chinedu ya fito. Wannan shi ne fim ɗin da aka fara sa ni. Ka ji ta yadda na fara sana’ar fim ɗin Hausa kenan, dalilin rawa.

FIM: A iya cewa duk wanda ya san Nasiru Horo ya san shi a ɓangaren barkwanci. Shin me ya sa ka zaɓi wannan fanni fiye da sauran?

NASIRU HORO: Ai ni ba a iya ɓangaren barkwanci na tsaya ba; na kan taɓa sauran fannonin. Da man ai idan ka tsinci kan ka a matsayin jarumi, to kamata ya yi a ce komai ka iya, duk inda aka taɓa ka ka iya.

To kuma gaskiya sai dai mu gode wa Allah a wannan masana’anta, don wallahi duk inda aka sa ni – kamar ɓangaren kwamedi ne ka ce in yi, zan yi, ko kuma na fito a ɓangaren sentimental ne ka ce na yi, zan yi. Kowane abu ka ce na yi zan yi, na ba ka abin da ka ke so. Saboda ba abin sauƙi ba ne ka tara mutane dubunnai cikin minti ɗaya ka ba su nishaɗi, wannan kawai baiwa ce ta Allah.

Kamar yadda kuma na faɗa maka tun a baya cewa na taso ne a matsayin yaron marigayi Ibro, tun daga nan ne na fara ganin abin ya ƙara burge ni da kuma shiga rai na, don ko wata ran idan na yi abu a cikin fim na dawo ina kallo sai abin ya ban mamaki har ina tambayar kai na cewa da man ni na yi wannan abin? Sai in yi ta mamaki. Sannan kuma Allah ya yi sai na ci abinci a wannan harkar. Shi ya sa na ke yi wa Allah godiya da wannan lamari.

FIM: Sau da dama al’umma na faɗin cewa tun rasuwar Ibro harkar barkwanci ta taɓarɓare. A matsayin ka na matashi kuma rainon Ibro, wane ƙoƙari ka ke yi wajen ganin an ci gaba daga inda aka tsaya a harkar barkwanci?

NASIRU HORO: To maganar gaskiya, magana a kan barkwanci da ake cewa ta ja baya ba haka ba ne, sai dai a faɗa dai ga waɗanda ba su sani ba. Amma maganar harkar nishaɗi, gaskiya ba abin da ya ja baya sai dai ƙaruwa saboda ko yanzu da yawa daga cikin mutane in su na so su samu abin nishaɗi su kan yi ƙoƙarin kallon kwamedi, musamman yanzu da zamani ya sauya wanda mutum ɗauko wayar sa kawai zai yi ya zauna, cikin lokaci kaɗan zai ba ka dariya kuma ko ka na cikin ɓacin rai a lokaci kaɗan zai sa ka manta da wannan yanayin na ɓacin rai.

Sai dai yanzu a iya cewa zamani ya sauya akalar finafinan ne; saboda da za ka ga ana yin abin cikin sidi amma yanzu kuwa komai ya koma yanar gizo, kuma hakan ya sanya aka ƙara samun masu wannan harka ta barkwanci bila adadin. To don haka yanzu ma mu ka fara, ba batun tsayawa.

Nasiru Horo riƙe da satifiket ɗin karramawa da Ƙungiyar Ɗaliban Jihar Jigawa ta Ƙasa ta yi masa.

FIM: Mecece alaƙar ka da Adam A. Zango?
NASIRU HORO:

Ni dai Horo Ɗanmama a harkar fim ɗin Hausa gaskiya a yanzu ba ni da wani maigida sama da Adam A. Zango, kuma ina alfahari da shi sosai a duk inda na je a rayuwa ta. Kuma alaƙar ce ta sa wasu su ke kira na Amanar Adam A. Zango, saboda ya ba ni yarda fiye da tunanin mai tunani.

Kai, akwai abin da idan na aikata aka gaya wa Adamu ba zai yarda da cewa ni ne na yi ba. Amma kuma akwai abin da ana cewa Horo ya yi, musamman rashin kunya, zai ce zan aikata, in dai ta wannan fannin ne zai yarda. Ko kuma (a ce ni) mai faɗar magana ne gatse-gatse, in ta zo kawai faɗa na ke saboda wani lokacin baki na ba linzami, to kawai zai ce hali na ne. To gaskiya alaƙa ta da shi ba za ta misaltu ba.

FIM: Ya ka ke ji a lokacin da ka haɗu da masoyan ka?

NASIRU HORO: Ina matuƙar jin daɗi sosai da sosai saboda kai ne ka ke ta roƙon Allah ya haɗa ka da masoya Allah kuma ya bada. Ka ga in Allah ya ba ka me za ka yi? Sai kawai ka tarairaye su, ka ji daɗi.

Hana rantsuwa, wallahi idan na je wuri na ji ana wane ne wane ne, wani daɗi ne maras misaltuwa ya ke ziyarta ta. Wani wajen ma idan na lura ba su gane ni ba, da gayya za ka ga na tsaya na yi musu sallama don idan wani ma ya na ma wata fahimta sai ya san cewa kai ba kowa ba ne, yadda wane ya ke ni ma haka na ke. Ba wani zancen wata ɗaukaka, Allah ne ya ke kai kowa.

FIM: A ƙarshe, menene kiran ka ga masoya ko jan hankali?

NASIRU HORO: Ni dai ba abin da zan ce da masoya na sai dai godiya. Allah ya saka da alkairi kuma Allah ya ƙara mana son Annabi.

Sannan ina ƙara gaya wa masoya na cewa ku ci gaba da bibiya ta da kallon abubuwa na na nishaɗi da na ke muku da kuma waƙoƙi na da na ke yi muku a shafi na na YouTube domin ni naku ne har a gobe.

Nasiru Horo: Ba ni da ubangida da ya wuce Adam A. Zango.
Dan Allah Ku Tura Zuwa Facebook WhatsApp Instagram Twitter And Telegram.

- Advertisement -