Adadin Fasinjojin Jiragen Kasa Na Sin A Ranar 1 Ga Wata Ya Kai Matsayin Koli A Tarihi

0
63

Adadin Fasinjojin Jiragen Kasa Na Sin A Ranar 1 Ga Wata Ya Kai Matsayin Koli A Tarihi

Daga CRI Hausa

Alkaluman da kamfanin layin dogo na kasar Sin ya fitar solar nuna cewa, jiya ranar 1 ga wata, wato rana ta farko ta bikin hutun ranar ‘yan kwadago ta duniya, gaba daya adadin fasinjojin da suka shiga jiragen kasa a fadin kasar ya kai miliyan 18 da dubu 826, adadin da ya karu da kaso 9.2 cikin dari kan makamancin lokacin shekarar 2019, kuma ya kai matsayin koli a tarihi.
Yau ranar 2 ga wata, an yi hasashen cewa, adadin fasinjojin zai kai miliyan 14.2, wato zai karu da kaso 7.7 cikin dari kan makamancin lokacin shekarar 2019. Hukumomin da abin ya shafa na kamfanin layin dogon kasar Sin solar yi kokari matuka domin biyan bukatun fasinjojin. Adadin jiragen kasar fasinsoji solar kai 11416 a jiya, a cikinsu, jiragen kasa da aka kara solar kai 1624, yau an kiyasta cewa, jiragen kasa za su kai 10739, kuma jiragen kasa da za a kara za su kai 1081.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

What's On Your Mind?