Abubuwan Da Ba Ku Sani Ba Game Da Mutuwar Auren Bill Gates Da Melinda

- Advertisement -

Abubuwan Da Ba Ku Sani Ba Game Da Mutuwar Auren Bill Gates Da Melinda

Daga Khalid Idris Doya

A farkon makon nan ne rahotonni suka bazu da ke cewa fitaccen mai kudin nan na duniya wato Bill Gates ya sake matarsa Melinda bayan da suka shafe shekaru 27 a tare.

Mutuwar aurensu ya baiwa al’ummar duniya sosai mamaki wanda ya zama abun tattaunawa da muhawara mai zafi a fannoni daban-daban musamman a kafafen sadarwa na zamani, sai dai su mashahuran masu kudin biyu solar bayyana da kansu cewa solar gano cewa ba za su iya cigaba da zamantakewar aure a tare ba ne, wannan dalilin ne ya sanya suka dauki matakin rabuwa kawai domin kowa ya huta da juna.

Kasancewar Bill da Melinda solar yi hadaka na tsawon lokaci a fannin kasuwanci da Gidauniyarsu ta Bill Gates, tunin rahotonni suka fara nuni da cewa Bill har ya fara sake ma Melinda wasu daga cikin ababen da suka kasance ribarta ko a ce hakkokinta na daga tarayyar kasuwanci da suka yi.

Abun da jama’a ba su sani ba shine, bayan kasancewarsu ma’auta, solar kulla alaka ta kasuwanci da gidauniya mai karfi wanda kasashe da dama suka amfana da gidauniyarsu.

Bill Gates shi ne mutum na hudu mafi arziki a duniya, a cewar mujallar Forbes, ya mallaki $124bn (£89bn), sannan yayi amfani da dukiyarsa wajen kafa gidauniyar da ke bada gudunmawa wajen cigaban fannonin rayuwa.

Ya samu kudadensa ne ta hanyar kamfanin Microsoft a 1970, kamfanin manhaja mafi girma a duniya.
Melinda ta soma aiki a Microsoft a matsayin manaja a 1987, kuma a wannan shekarar mutanen biyu suka zauna domin tattaunawa a liyafar cin abinci a New York.

Daga nan soyayya ta shiga tsakani, amma kamar yada Bill ya shaida wa wani shirin Netflid: “Mun damu da juna sosai kuma sai ya kasance mun shiga wani yanayi na zabi biyu: wato, ko mu rabu ko mu yi aure.”
Melinda ta ce ta tsinci Bill cikin wani yanayi na tababa a zuciyarsa yana nazari da rubuce-rubuce kan alfanu da rashin alfanun yin aure.

Solar yi aure a 1994 a tsibirin Hawaiian da ke Lanai, rahotanni na cewa solar yi hayar dukkanin jirage helikwafta domin hana bakin da ba a gayyata ba isa gare su.
Bill Gates ya bayar mukaminsa na Microsoft a shekarar da ta gabata domin mayar da hankalin kan ayyukansa na agaji.

Bincike ya nuna cewa ma’autan biyun suun hadu ne a shekarun 1980 lokacin da Melinda ta soma aiki a kamfanin Microsoft mallakin Bill din, ma’ana dai solar hadu ne a yanayin da take matsayin ma’aikaci a karkashinsa.

Bayan da suka yi auren, solar samu haihuwar ‘ya’ya uku.
A wani sakon da suka wallafa a shafin yanar gizo na Tuwita, mashahuran masu kudin biyu solar nuna cewa, “Bayan dogon nazari mai zurfi da muka yi a tsakaninmu da kokarin daidaita zamanmu, mun yanke shawarar kawo karshen aurenmu, ma’ana mun rabu.”
Tsoffin ma’auratan biyu dai sune ke tafiyar da fitaccen Gidauniyar Bill da Melinda Gates da ke taimakawa a sassa daban-daban na duniya ta fannoni daban-daban.

Gidauniyarsu ta kashe biliyoyin daloli wajen yaki da cutuka da karfafa rigakafi ga yara. Gidauniyar da mai zuba jari Warren Buffett ta samar da wani tsarin tallafi, da ke kira ga attajirai su mayar da hankali wajen fitar da kaso mai yawa na arzikinsu a fannin ayyukan ci gaba.
Ma’auratan biyu solar ce: “Sama da shekaru 27 na auratayarmu, mun haifa da tarbiyar da yara uku da kafa gidauniyar da ke aiki a ko ina a duniya domin taimaka wa mutane samun ingantacciyar lafiya, da rayuwa mai inganci. Mun amince cewa za mu ci gaba da aiki tare domin cimma muradanmu da ayyukan gidauniyarmu, amma mun yarda cewa ba za mu iya ci gaba da rayuwa tare a matsayin ma’aurata ba.

“Mun nemi saukakawa juna saboda iyalinmu yayin da muke shirin soma sabon babi a rayuwarmu,” a cewarsu a shafinsu da suka wallafa.
A shekarar da ta gabata ne aka yi baikon auren diyarsu wacce take daya daga cikin ‘ya’yansu uku da suka haifa.
diyar fitaccen mai kudin duniyar nan Bill Gates, Jennifer ta sanar da cewar an yi baikonta da masoyinta dan kasar Masar, Nayel Nassar.

Jennifer da Nassar na soyayya tun a shekarar 2017 sannan suka yi baiko a wani wasan sululun cikin kankara da suka halarta.

Masoyan na wasanni irin na tsalle-tsalle da hawa doki suna kada su cikin duwatsu, sannan solar yi wasanni da dama tare a fadin duniya.
Jennifer, ta sanar a shafinta na Instagram cewa, ta kosa ta ga lokacin da za su karasa rayuwarsu tare suna daukar darasi daga wurin juna, su rayu tare suna nishadi da soyayya.

Nayel a nasa shafin ma ya wallafa cewa, “Na kagu mu ci gaba da rayuwa tare, sannan ba na tunanin rayuwa ba tare da ke ba”. Jennifer Gates mai shekara 23, daliba mai koyon aikin likitanci kuma mai son hawa doki a hirarta da kafar yada labarai na CNN, ta ce saurayinta na ba ta goyon baya ta kuma kara da cewa yadda suke son dawakai abu ne mai ban sha’awa.

- Advertisement -