Bidiyo: Abubuwan al’ajabi da baku sani ba game da Shugaba Buhari

0
82

A duk lokacin da aka fara magana a kan tarihin Najeriya, dole ne a kira sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hakan ta kasance ne sakamakon rawar da ya taka a wasu muhimman abubuwan da suka faru kuma suka sauya akalar kasar nan baki daya.

Daga zamansa shugaban kasa a yayin mulkin soja har zuwa rike shugabancin PTF da yayi, da kuma zamansa shugaban kasa a karkashin mulkin fara hula.

Dole a ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zarra cikin sa’o’insa da kuma sauran takwarorinsa a duniya.

Ga bidiyon wasu abubuwan al’ajabi da baku sani ba game da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bidiyo: Abubuwan al'ajabi da baku sani ba game da Shugaba Buhari

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.

Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.

Bai Wa Gwamnati Goyon Baya Ne Zai Bata Kwarin Gwiwar Samun Nasara -Injiniya Amshi

Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga ‘yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai. Shugaban kasar ya kara da amincewa da cewa, kasar na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban a sassan kasar.

Ya ce, “A yau na tabbatar da cewa Najeriya tana cikin mawuyacin hali na tattalin azriki kuma hakan ce ta kasance ga kowacce kasa a fadin duniya. Muna fuskantar kalubalen tsaro a sassa daban-daban na kasar nan.”

What's On Your Mind?