Abubuwa Bakwai Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabon Sarkin Zazzau

0
60

Sabon Sarkin Zazzau na 19, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli, jika ne daga gidan Malam Musa Bamalli, wanda ya karbo tuta daga Shehu Usman Dan Fodio, kuma Sarkin Zazzau na farko, wanda ya yi sarautar ta Zazzau daga shekarar 1804 zuwa 1821.

Mahaifinsa, H.E. Nuhu Bamalli, ya rike mukamin sarautar Magajin Garin Zazzau, watau mukami na biyu a jerin masarautar Zazzau har na tsawon shekaru 40.

Abubuwa Bakwai Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabon Sarkin Zazzau

Mal. Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi aiki a matsayin mukaddashin Magajin Garin na Zazzau, a inda yake wakiltar mahaifinsa a wuraren taruka har na tsawon shekaru 20. An kuma naxa masa rawanin Magajin Garin ne a shekarar 2001, a sakamakon mutuwar mahaifin na shi.

Ta fuskacin mahaifiyarsa kuma, shi ya kasance jika ne kai tsaye na shahararren malamin addinin Musulincin nan Shehu Usmanu Danfodio.

Ahmed Bamalli Ya Zama Sarkin Zazzau

Mahaifiyarsa xiya ce ga Abdurrahman Dikko, da kuma jikanyar nan ta Sarkin Musulmi Aliyu Babba da Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, da kuma Shehu Usman Danfodio.

A yanzun haka kuma shi ne jagoran gidan sarautar na Mallawan Zazzau.

Har ya zuwa lokacin naxin na shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19, Bamalli yana rike ne da sarautar Magajin Garin Zazzau.

What's On Your Mind?