Hukumar rarraba wutar lantarki ta Kaduna ta yanke wutar gidan tsohon shugaban kasa marigayi Shehu Shagari saboda bashin naira miliyan 6 da ake bin gidan.
A ranar 28 ga watan Disamba ne 2018 tsohon shugaban ya rasu yana da shekara 93.
Jaridar DAILY NIGERIA ta rawaito kakakin kamfanin, Abdulaziz Abdullahi na cewa ba a biyan kuɗin wutar tun bayan mutuwar marigayi Shagari.
Kakakin ya kuma shaida wa jaridar cewa an basu wa’adi ko ɗaga musu ƙafa domin biyan kuɗaɗen da ake bin su kafin a yanke wutar.
Wani jami’in gwamnatin jahar Sokoto wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce babu adalci idan aka ɗaurawa gwamnati laifi kan yanke wutar, a cewar Jaridar.
Allah sarki duniya, lallai kasar nan duk wanda yayyi aiki akan gaskiya sai dai ya jira sakamakonsa a lahira, amman da zarar ya mutu za a manta da shi, za a manta da ya’yansa.
Tabbas wannan abin kunya ne ga gwamnatin jahar Sokoto da kuma masu kudin jahar Sokoto. Majiyarmu ta samu labarin ne daga nasara.
369 total views, 3 views today
Be the first to comment