Abduljabar Yayi Martani Bayan Haramta masa Karatu a Kano

0
82

ccen malamin Musulunci a Jihar Kano, Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara ya mayar da martani kan rufe masallacinsa da majalisinsa da Gwamnatin Jihar Kano ta yi bisa zargin sa da yin batanci ga Sahabban Manzon Allah (SAW).

Malamin ya mayar da martani ne ’yan sa’o’i bayan Gwamantin Jihar ta sanar da matakin tare da haramta masa gudanar da karatuttuka ko gabatar da lacca ko ko huduba ko sanya karatuttukansa a kakafen yada labarai har sai an kammala bincike.

Abduljabar Yayi Martani Bayan Haramta masa Karatu a Kano

Kadan Daga Aika-aikar Abduljabbar kabara Goma Sha Hudu Ga Sahabbai Da Manzon S.a.w

Kamae yadda Aminiya na wallafa a shafin ta. A tattunawarsa da Sheikh Abduljabbar ya ce matakin da gwamnatin ta dauka a kansa ya tabbatar masa da cewa a kan gaskiya yake, kuma malaman da ke zarginsa da kagen karatu ba su da abin fada.

“In da abin da na ji shi ne tabbatatar kasancewata bisa gaskiya, domin ba da gwamnati nake magana ba da malamai nake; ya zama karshe gwamnati ce ta amsa musu, wannan sai ya nuna mini malamai ba su da amsa.

“A matsayina na almajiri, maganar da nake yi ta ilimi ce da malamai, ya zama mai ban amsa ita ce gwamnati ce take amsa musu, ya nuna malamai ba su da amsa,” inji malamin.

What's On Your Mind?