A Yi Amfani Da Azumin Ramadan Don Yi Wa Nijeriya Addu’a – Gwamna Bagudu 

- Advertisement -

A Yi Amfani Da Azumin Ramadan Don Yi Wa Nijeriya Addu’a – Gwamna Bagudu 

Daga:Umar Faruk,

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da watan azumin Ramadana, don yin addu’ar Allah mai karfi, don ceto kasar Nijeriya daga tarin matsalolin da suka dabaibaye kasar, musamman ma kalubalen tsaro da ke faruwa a jahohin kasar nan.

Gwamnan Jihar, ya yi wannan kiran ne, yayin da yake karbar bakuncin wasu bangare na Ma’aikatan Gwamnati, wadanda suka hada da bangaren shari’a da ‘yan majalisu da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya da na Jihar, wadanda suka kawo ziyarar a fadar gwamnatin Jihar a Birnin Kebbi, don buda bakin azumin watan Ramadana jiya.

Sanata Abubakar Atiku Bagudu yayin da yake godiya ga dukkan wadanda aka gayyata saboda halartar shan ruwa azumin Ramadan tare da shi, ya yi kira ga al’ummar da su rukunin ‘yan Najeriya da su rike imaninsu da kuma yin addu’oi, don neman yardar Allah. Haka kuma ya ce” jama’a mu nemi tsarin Allah don tserar da kasarmu daga munanan ayyukan ‘yan fashi da sauran mutanen da ba su ji ba, ga halaka.

Gwamna Bagudu ya nuna bacin ransa kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar Nijeriya, wanda a cewarsa kara tabarbarewa lamuran tsaro yana da nasaba da amfani da miyagun kwayoyi, rashin hakuri da rashin hakuri a tsakanin junna.

Bugu da kari ya yi kira ga matasa a kasar nan, da su guji shan haramtattun kwayoyin saboda ba su da wata tasiri ga lafiyarsu da kasarsu, zai dai haddasa rashin tsaro da rashin Zaman lafiya. Wanda Shi ne kasar nan ke fuskantar.

‘”Abin da muke fuskanta a yau shi ne haduwar itan ta’adda da shan ƙwaya, hade da rashin haƙuri da juna.

“Dole ne mu kasance masu yin addu’a ga kasarmu ta masoya, mu yi hakuri da juna, ba tare da nuna kabilanci da addini ba,” in ji shi.

 

Har ilayau, Gwamnan ya ce” lokacin da muke ciki lokaci ne da kasar Nijeriya ke bukatar addu’o’in ‘yan kasa don samun cikaken Zaman lafiya.

Yayin da yake kokawa kan ayyukan ta’addancin ‘yan fashi a wasu yankuna na masarautar Zuru, Gwamna Bagudu ya ce, gwamnatinsa na daukar matakai da dama don shawo kan zaman lafiya da tsaron mutane a yankin.

‘Yan bindiga solar shigo jihar Kebbi daga jihar Zamfara da Neja don haifar da rikici a cikin al’ummomin mu.

“A da, ‘yan fashin suna zuwa daga Mali, suna wucewa ta Bachaka, a karamar hukumar Augie, amma hakan ya zama tarihi a yanzu, har ma da wannan matsalar da muke fuskanta yanzu za a shawo kanta In Sha Allahu, “in ji shi.

Daga nan Sanata Bagudu ya kuma shawarci al’ummomin da ke son kafa kungiyoyin ‘yan banga da su yi hakan ba tare da sabawa doka ba, sannan ya yi kira ga’ yan siyasa da su daina sanya siyasa a harkokin tsaro.

Ya kuma gargadi ‘yan Nijeriya, da su ci gaba da baiwa wannan gwamnati goyon baya don shawo kan matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.

Nijeriya ya ce, kasa ce da Allah Ya albarkace ta da wadatattun mutane da albarkatun arziki kasa, wanda dole ne a yi amfani da shi sosai don ci gaban dan Adam.

Da yake jawabi tun da farko, Kwamishinan filaye da Gidaje, Honorabul Muhammad Mamuda Wara wanda ya yi Magana a madadin wadanda aka gayyata, ya gode wa Gwamna Bagudu bisa karbar bakuncinsu don buda baki tare da shi.

Wara ya yaba da irin kokarin da Gwamnan ke yi na ci gaba da bunkasa kayayyakin jihar gaba daya, a cewarsa, za a iya samun ci gaba.

Daga cikin wadanda suka halarci buda baki na buda, akwai Shugaban Ma’aikata, a Gidan Gwamnatin Jihar Kebbi, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu (Jarman Kabi), Kwamishinan Zabe na Jihar Kebbi, Alhaji Ahmed Bello Mahmud, Dokta Haliru Bala na Hukumar kidaya ta kasa. , Alkalai, Khadis, Kwamishinoni da Wakilan Majalisar dokoki.

- Advertisement -