A Siyasance Ba Za A Zargi Gwamnatin Buhari Da Kasawa Ba Kan Tsaro – Kungiyar Ciki Da Gaskiya

- Advertisement -

A Siyasance Ba Za A Zargi Gwamnatin Buhari Da Kasawa Ba Kan Tsaro – Kungiyar Ciki Da Gaskiya

Daga Ibrahim Muhammad Kano.

Malam Mustapha Aminu Yusuf marubuci mai sharhi akan al’amuran al’umma, dan gwagwarmayar siyasa wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar Ciki da Gaskiya da suke amo a kan kare manufofin Gwamnatin Buhari ya bayyana
lamarin tabarbarewar tsaro da cewa tana sanya damuwa a zukatan masu kishin kasar nan.
A cewarsa da zarar matsalar tsaro ta shigo duk abinda za a yi na maganin ta sai an dau lokaci. Musamman a nan Nijeriya ya ce matsalar ta yi ta’azzarar da duk abin da za a yi na maganceta da rageta da kawo karshenta sai ya dauki lokaci, saboda matsalar ta zama ta abubuwa daban daban.
Ya ce, “Da farko dai a siyance ba za a zargi Gwamnatin shugaba Buhari da kasawa ba, dan abin nan ba lokacinsa aka soma shi ba, abu ne da ya gada daga gwamnatin da aka fara a wurinta, ita mai ya sa ba ta yi maganinsa ba? A lokacin gwamnatin baya akwai wasu yankuna na kasar nan da ke karkashin ‘yan ta’adda sai da  aka sami kananan hukumomi 17 a karkashin Boko haram. A lokacin dansanda a nan Kano bai isa ya sa kayan sarki ba, yawanci ofisoshin ‘yan sanda an rufe. Wannan a bangaren ‘yan ta’addar Boko haram kenan.
“Haka a bangaren garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda su ma daban suke. Su masu garkuwa da mutane wata matsala ce ta neman kudi da mutanen da aka kassara rayuwarsu a dazuzzuka wato Fulani saboda cinye burtalai da wurin kiwonsu da kuma kabilanci da bambancin addini da ake nuna musu, wasu abubuwa ba lokacin Buhari aka soma ba, an dade aka yi ta yi har girma, wadanda za su yi maganin abin da wuri ba su yi ba, ta zo ta kwabe da wancan da aka  fara lokacin PDP ta hadu da wannan.
“Sai yan ta’addar daji da ya samo asali daga hakar danyan gwal, wanda wasu mutane ne masu karfi da isa suke so su kwace wa gwamnati inda ma’adinai suke suka sayo makamai suke rabawa mutane a cikin dazuzzuka su tsare musu wajen su kwashi abinda suke so.” In ji shi.
Ya kara da cewa, “Kafin wannan, lokacin kasarnan ana cikin mawuyacin hali na talauci ga rashin aikin yi da wadannan abubuwa suka kwabe. Muhammadu Buhari Allah ya dora shi a kan mulkin kasar nan da take hannunsa a  wannan lokaci. Dan haka abin da yake na maganin matsalar tsaro ba gwamnatin da ta yi irinsa amma saboda girman lamarin sakamakon da yake samu sai ya zama kadan ne, mutane ba za su gani a yanda sukeso ba.”
Ya ce a wadannan abubuwa na tsaro an shigar da siyasa da don zuciya da jahilci na fahimtar me yake faruwa, “Siyasa ta shiga saboda wadanda Buhari ya karbe wa mulki ya zama yanzu ba ga hannunsu yake ba. kuma suna so su dawo da mulkin a hannunsu, dan haka suna  duk abin da za su yi su nuna wa mutane Buhari ba ya komai suna yi za su gaya wa mutane bai damu da kula da abinda ya dame su ba, saboda  siyasa, Ita kuwa siyasa don kar mutane su saurare ka, sai a shigar da son zuciya. Ba a duba me Shugaba Muhammad Buhari ya yi sai a dinga duba matsala Kuma ina tabbatar maka Buhari ya damu da wannan hali da ake ciki yana kokarin kawo karshenta.” In ji shi.
Malam Mustapha Aminu  ya ce ba a taba yin lokacin da ake kulawa da jin dadi da walwalar sojoji kamar a  Gwamnatin Buhari ba, “Ga albashinsu yana zuwa kan kari, wannan karfafa tsaro ne, dan in aka karfafe su da kayan aiki da walwala shi ne za ka karfafi tsaro. Ba a taba sayen makamai da kera makamai da motocin soja  a kasar nan kamar wannan lokaci ba.
“Kuma duk abinda ake yanzu ba  za a ce a ga  sakamako yanzu ba. Amma abinda ke aukuwa yanzu ya nuna ana samun nasarori a ciki kullum ana fasa ‘yan ta’addan Sambisa suna gudu an datse hanyoyinsu na samun makamai dana abinci duk solar fito daga daji kuma hade katin dan kasa da ake da lambar  waya yana tona musu asiri ana ganinsu a kama su a duk  inda suke guduwa a bangaren yaki da ta’adda cin boko haram ko mutum ba ya gani ya ji nasarorin da ake samu.”
Malam Mustapha ya ce wasu abubuwa dake dabaibaye tsaro a kasarnan shi ne siyasa knowledge shiga, “dan  akwai manyan mutane a wannan harka ta ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane, akwai ‘yan siyasa manya wadansu ma na rike da mukaman gwamnati wadanda suna cikin wannan abu kuma ba sa so ta kare. Wannan ita ce babbar matsala. Da a ce wancan bangaren na kishin al’umma yanda Bihari yake da sai a hadu gaba daya a yi maganin matsalar, amma wasu suna ta’azzara matsalar wasu na kokarin ta cigaba da habaka, wasu na ciki ana yi da su  domin kawai  a bata Gwamnatin Buhari asa ka da mutane su fahinci kishinda yake yi ga al’umma.
Ya ce bincike da wata cibiya ta yi nemi a binciki jam’iyyar PDP dan akwai zargin da  hannunta a wasu abubuwa da ake yi na ta’addanci a kasar nan.
Ya ce “akwai wani  tsohon sanata da aka samu da, yake yin  fashi da makami a Kwara lokacin yana sanata  aka tarar yaran sa ne suka yi fashi da makami da tsakar rana a titi wajen  mutum 56 suka kashe  motar gwamnatice ta raka su da ita suka yi fashin.
Cibiyar “brigeta” ta bada labari  akwai kudin Naira Biliyan 100 da PDP ta ajiye na sayen makamai, da za a duba wannan cikin idon basira a yi bincike a tabbatar da wannan magana ta   cibiyar “Brige”ai da PDP ta rasa halascinta na zama jam’iyya a kasar nan domin ta sabawa tsarin mulki. Tsarin mulkin kasa ya hana jam’iyyar siyasa ta yi mu’amala da makamai. An yi wannan zargi a bincika a tabbatar idan PDP tana da hannu a matsalar tsaro da ta shafi Nijeriya a yanzu a duba in har tana da hannu to ya zama wajibi a janye rijistarta ba jam’iyyar siyasa ba ce, saboda ta saba wa tsarin mulkin kasa wanda ya haramta jam’iyyar siyasa ta yi wata mu’amala da makamai ko ta horas da wadanda za su yi amfani da makamai ko ta goya musu baya wannan shi ne abin da gwamnati yakamata ta yi dan tabbatarda gaskiya.” In ji shi.

- Advertisement -