A Masallatan Juma’a Za A Yi Sallar A Abuja Ba A Na Idi Ba, In Ji Minista

- Advertisement -

A Masallatan Juma’a Za A Yi Sallar A Abuja Ba A Na Idi Ba, In Ji Minista

Daga Idris Aliyu Daudawa

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Malam Muhammad Musa Bello, ya ba da umurnin cewa mazauna garin Abuja kowa ya yi sallar Idi a Masallacin Juma’a mafi kusa da shi, a maimakon zuwa masallatan idi.

Ya bayyana haka ne a taron da ya shugabanta na tawagar Limaman Abuja, a karkashin Shugabanta  Imam Tajudeen M.B Adigun, domin su tattauna yadda za a gudanar da Sallar Idin mai zuwa.

A na shi jawabin Ministan ya godewa Shugabannin addinin kan hadin kan da suka badawa, a fafutukar da ake yi ta yaki da cutar Korona, inda kuma ya ce tunda aka fara kammalawa da lokacin information bulla har aka rufe wurare masu yawa, sai kuma shi karo na biyu wanda shi aka fi haduwa da matsaloli, na karuwar wadanda suka kamu da cutar. Don haka yana dakyau a dauki wasu matakan domin kaucewa shiga wani al’amarin nata na uku, kamar yadda wasu kasashe ake ganin suke ta fama da matsalar.

Bugu da kari kuma kamar dai yadda jam’ai daga Sakatariyar kula da lafiyar al’umma ta babban birnin tarayya da kuma aiiwatar wadanda suka yi jawabai da kuma aiwatar da tsare- tsaren wadanda suka kunshi, takaita tafiye- tafiye wanda kwamitin kula da ana bin dokokin hana yaduwar cutar, wanda ya yi zaman shi ranar Litinin 10 ga watan Mayu 2021, an dauki wadannan matakan.

Ba za ayi Sallar Idi ba a wurin da aka saba yi dake kan titin Umaru Musa ‘Yar’dua   na hanyar  zuwa filin jirgin sama.

Dukkan masallata ana bukatar su yi Sallolinsu a masallatan Juma’a, da suke kusa dasu.

Kada kuma su kai kashi hamsin na yawan mutanen da wurin zai iya dauka.
Shugabannin kulawa da al’amuran musulunci ana shawartar su da su kula da yadda mutanen suke shiga masallatan.

Ya kuma dace a kula da kuma kiyaye dukkan abubuwan da aka saba yi tun lokacin da cutar ta Korona ta bulla, kamar sa takunkumin fuska, bayar da tazara, da kuma wanke hannuwa.

Duk wadansu bukukuwan muranr Sallar ya kamata ayi su a gida, tunda duk ma wuraren shakatawa da holewa za a kulle su.

A karshen taron Shugaban ba kungiyar ta Limaman na babban birninm tarayya Drakta Tajudeen Mohammed Bello Adigun, wanda ya yi magana  a madadinsu ya bayyana cewa “A musulunci ya dace a saurari kwararru wadanda suka san abu, wadanda suka tatauna da mu ko shakka babu kwararru ne a bangaren daya shafi kula da lafiyar al’umma, da yadda za a bullo ma rashin lafiyar ko cuta a kimiyyance. Hakanan ma musulunci ya dace da abi ko kuma yi amfani da ka’idojin da shugabanni suka bayar”.

Daga karshe Dakta Adigun ya bayyana cewa “ Saboda dalilan da  suka bayyana da kuma hujjoji mun gamsu kwarai, muna kuma yin kira da ‘ya’uwa al’ummar musulmi suma da su yi biyayya kan matakan da ita hukumar babban bbirnin tarayya ta dauka, ta mu hakura mu yi Sallar Idil- Fitir a wuraren da muke zama.”

- Advertisement -