A Baya An Fi Shan Wahala Kafin A Yi Suna A Fim – Nafisa Ishak Rano

- Advertisement -

A Baya An Fi Shan Wahala Kafin A Yi Suna A Fim – Nafisa Ishak Rano

Daga Saddik Muhammad a Kano.

Daya daga cikin jarumai mata da su ka dade ana damawa da su a masana’antar finafinai ta Kannywood, wadda kuma a yanzu take ganin burin ta ya kusa cika na zama fitacciyar jaruma ta nuna karfin gwiwar da take da shi a yanzu na kaiwa matakin babbar Jaruma wadda ta dade tana burin kaiwa.

Jarumar wadda ta shafe kusan shekaru sha daya a cikin masana’antar ta yi wa wakilin mu bayanin abubuwa da ta gani a cikin harkar fim a lokacin da suka tattaunawa. Amma dai da farko mun tambaye ta tarihin rayuwar ta ne in da ta fara mana da cewar.

“To ni dai suna na Nafisa Ishak Rano, kuma ni haifaffiyar garin Rano ce a ke cikin jihar kana, an haife ni a shekarar 992, kuma na yi makarantar boko a garin Kano har zuwa matakin Sakandare, sannan na yi makarantar Islamiyya duk dai a nan garin Kano, kuma na yi aure a 2014,shekara ta uku muka rabu da miji na muna da yaro daya.

Nafisa Ishak Rano

To ko yaushe kika fara harkar fim
Na fara harkar fim ne a 2010, kuma abin da ya jawo hankali na shi ne daman tun asali ina da sha’awar shiga harkar fim saboda gudummawar da na ke ganin masu harkar fim suna bayarwa hakan ya sa nima na ga ina bukatar na shigo don nima na bayar da tawa gudummawar to wannan shi ne ya jawo hankali na cikin harkar, kuma fim din da na fara da shi, shi ne fim din Kawalliya, da kuma Ibro Dan karota, sai kuma rayuwar Amina, sai kuma wanda na ke yi a yanzu shi ne Surukan zamani.

To ko wa ye ya yi miki hanyar shiga harkar fim?
Wanda ya yi mini hanyar shiga harkar fim dai shi ne Mairafas wanda a yanzu Allah ya yi masa rasuwa, ta hanyar sa na shigo harkar fim kuma har ya sa aka sanni a cikin harkar.

Daga cikin finafinan da kika yi ko akwai Wanda ke ce kika zuba kudi kika dauki nauyin shirya shi a matsayin Furodusa?
E gaskiya haka ne, domin fim din Kawalliya ni na zuba kudi na shirya shi.

Finafinan da kika yi suna da yawa tun daga shigowar ki zuwa yanzu?
To gaskiya zan iya cewa ba su da yawa sosai don ba su fi Hudu zuwa biyar ba, sai dai a yanzu na na samu shiga cikin shirin Dadin Kowa kuma ina yin. Wakoki wanda a yanzu su na fi yi ma.don haka ina sa ran nan gaba na cimma nasarar da na ke nema a cikin harkar fim.

Ya kike ganin ci gaban da aka samu a yanzu?
To gaskiya ana samun ci gaba sosai ba kamar a baya ba, domin a baya an fi shan wahala sosai kafin mutum ya samu a san shi a matsayin jarumi musamman mata sai a yi ta shan wahala ba tare da an san mutum ba sai mai tsananin rabo, amma a yanzu sakamakon ana yin wakoki kuma suna da tasiri sosai, yanzu ko a waka ma sai jaruma ta yi suna ko ba ta fitowa a fim, don haka an samu ci gaba da sosai.

Wanne irin Matsaloli kika fuskanta a matsayin ki na mai harkar fim?
To, matsaloli dai suna da yawa ba za su lissafu ba, kamar yadda kowacce harkar rayuwa take da Nasarori masu yawa haka take da Matsaloli masu yawa don haka ita rayuwar Duniya ba ta rabuwa da Nasarori da Matsaloli.

A yanzu me kika sa a gaba ta bangaren buri a harkar fim?
To burina dai na gaba bai wuce na samu kaiwa ga matsayin da kowacce jaruma take son ta zama ba, wato na zama fitacciyar jaruma da kowa ya ke son ya gani ba, kuma ina fatan Allah ya kai ni ga wannan matsayin.

Menene sakon ki na karshe?
Sako na dai shi ne Ina yi wa kowa fatan alheri Allah ya bar mu tare da masoyan mu.

To madalla mun gode
Nima na gode sosai.

- Advertisement -