30 Daga Mutum 40 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Jihar Katsina Sun Kubuta

- Advertisement -

30 Daga Mutum 40 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Jihar Katsina Sun Kubuta

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kubutar kimanin mutum 30 cikin 40 da ‘yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke karamar hukumar Jibiya. An sace mutanen ne lokacin da suke gabatar da sallar Tahajjud ta dare.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru da tsakar daren yau Litinin ne, inda ‘yan bindigar da ba a tantance yawansu ba dauke da makamai suka kutsa cikin sabon masallacin da ke Unguwar Kwata.

A cewarsa, “lokacin da suka je solar yi harbe-harbe a sama kuma solar kwashi masallata wadanda suka fito domin yin sallar Tahajjud.”

Ya ce; bayan solar samu rahoton ne jami’an tsaro da yan kato-da-gora da kuma al’ummar gari suka yi gangami inda suka bi yan bindigar abin da ya ba su damar kubutar da mutum 30 cikin wadanda aka sace.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa binciken da suka yi bayan kubutar da mutanen ya nuna cewa akwai sauran mutum 10 da ba a san inda suke ba.

- Advertisement -