2023: Yahaya Bello Ba Zai Iya Shugabancin Ko Gidan Gonar Aladu Ba –Deji Adeyanju 

- Advertisement -

2023: Yahaya Bello Ba Zai Iya Shugabancin Ko Gidan Gonar Aladu Ba –Deji Adeyanju 

Daga Yusuf Shu’aibu,

Wani babban lauya da ke Abuja mai Suna Deji Adeyanju ya yi wa Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello izgilanci bisa aniyarsa ta neman shugabancin kasar nan. Adeyanju ya bayyana cewa, Yahaha Bello ba zai iya ko shugabancin gonan aladu ba ballantana ya iya shugabancin Nijeriya gaba daya.

Yahaya Bello ya bayyana cewa, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2023, ba zai taba bai wa ‘yan Nijeriya kunya ba. Gwamnan ya kara da cewa, wasu ‘yan Nijeriya ne ke ta rokansa a kan ya tsaya takarar a shekarar 2023.

A nasa martanin, Adeyanju ya bayyana cewa Yahaya Bello ba zai taba zama shugaban kasar Nijeriya ba, domin gwamnan ya kasa kulawa da ma’aikata Jihar Kogi. Babban lauyan ya kara jaddada cewa, a duk Nijeriya babu wata jihar da ta fi Jihar Kogi mummunan shugabanci a halin yanzu. Adeyanju ya rubuta a shafinsa na tweeter cewa, “Yahaya Bello ya ce ‘ya Nijeriya ne suke ta matsa masa a kan ya fito takarar shugabancin Nijeriya a shekarar 2023, kuma ya nuna cewa ba zai ba su kunya ba.

“A nawa tunanin, Yahaya Bello ba zai iya ko shugabancin gonan aladu ba. Jihar Kogi ita ce jiha ma fi muni wajen shugabanci a Nijeriya. Ma’aikata jihar suna fama da yunwa saboda babu albashi.”

- Advertisement -