2023: Matasan Arewa Sun Gindaya Sharuddan Na Goyan Bayan Takarar Tinubu

0
158

2023: Matasan Arewa Sun Gindaya Sharuddan Na Goyan Bayan Takarar Tinubu

Daga Yusuf Shu’aibu

kungiyar matasa Arewa (AYCF), solar gindaya wa Bola Tinubu jagoran jam’iyyar APC, sharuddan kafin ta goyi bayansa na tsayawa takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2023. Shugaban kungiyar AYCF, Yerima Shettima ya bayyana cewa, sai yankin Arewa solar gamsu da dangantakarsa da sauran yankuna Nijeriya kafin ta yanke hukuncin goyan bayan aniyar Tinubu na tsayawa takarar shugabancin kasar nan.
Da yake zantawa da manema labarai, Shettima ya bayyana cewa, tsohon gwamnan Jihar Legas sai ya yi kokarin gudanar da dangantaka mai kyau da sauran yankunan Nijeriya kafin yankin Arewa ya mara masa bayar a kan aniyarsa ta zama shugaban kasar Nijeriya.
A cewar Shettima, “idan Tinubu yana son tsayawa takarar, akwai hanyoyi da za mu bi wajen sauraron shi. Idan ya shirya tsayawa takarar shugabancin kasar nan, to sai mun duba yanayin dangantakarsa da sauran yankunan Nijeriya da ke wajen yankin Kudu-Maso-Yammaci da yadda ‘yan Nijeriya da ke wajen yankin Kudu-maso-Yammaci suke daukarsa.
“Yadda yake kokarin yin kyakkyawan mu’amula da mutane da ke wajen yankin Kudu-Maso-Yammaci da kuma abin da yake kokarin bai wa ‘yan Nijeriya da ke wajen yankin Kudu-Maso-Yammaci. Za Mu tattauna a kan haka tare da zantar da hukuncin idan lokaci ya yi,” in ji shi.
Akwai jita-jita cewa, wai tsohon gwamnan Jihar Legas zai tsayar takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar at 2023. Duk da wannan jita-jita da matsillamba daga wasu ‘yan Nijeriya, Tinubu bai fito ya bayyana matsayinsa ba sport da tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben mai zuwa.
A kwanan nan ne jagoran jam’iyyar APC ya musanta batun ya bude ofishin yakin neman zabensa a garin Abuja. Tinubu ya bayyana cewa, a yanzu haka ya mayar da hankali ne wajen taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya sami nasarar a kan burikansa.
Makwanaki kadan da suka gabata, an samu rahoton cewa ya rarraba buhunan shinkafa guda 10,000 a yankin Arewa. An dai rarraba wadannan buhunan shinkafa ne ga ‘yan gudun hijira da ke Jihar Borno tare da hotonsa a jikin kowani buhun shinkafa. Sai dai Tinubu ya nisanta kansa da rabon wadannan shinkafa, wanda ya ce bai san wadanda suka aiwatar da hakan ba. Amma kuma duk da hakan, Tinubu ya yaba wa wadanda suka rarraba buhunan shinkafa mai dauke da hotunansa a jiki.

What's On Your Mind?