2023: Kungiya Na Neman Gwamnan Bauchi Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

- Advertisement -

2023: Kungiya Na Neman Gwamnan Bauchi Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

Daga Khalid Idris Doya,

Wata kungiyar ta bukaci gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da ya fito takarar shugaban kasar Nijeriya a zaben 2023, kungiyar tana mai cewa duba da irin kyakkyawar shugabanci da gwamnan ke shinfidawa a jiharsa akwai bukatar ya fadada gogewarsa zuwa ga illahirin kasar nan baki daya.

Kungiyar ta bayyana cewar Nijeriya tana cikin tsaka mai wuya wanda take tsananin bukatar nagartacce, gogagge kuma hazikin da zai ja ragamar kasar da za a kai ga nemo hanyoyin shawo kan matsalolin da suka hada da na tsaro, da na tattalin arziki da ke neman gurgujewa.

Shugaban kungiyar mai suna ‘Kaura Bauchi Physique Builders Affiliation’ Malam Dauda Mele shi ne ya yi wannan kiran a hirarsa da ‘yan jarida a Bauchi jiya.

Mele na cewa, “Zahirin zance Nijeriya na neman tsayayye kuma gogaggen shugaba, idan muka duba halin da muke ciki, Kauran Bauchi ya dace da Nijeriya domin kuwa ya tabbata mana shi shugaba ne mai ilimi, hangen nesa, matashi, masanin tattalin arziki da kuma yadda za a inganta tsaro.

“Lokacin da Bala Muhammad ya zama gwamnan Bauchi ya karbi mulkin jihar yayin da tattalin arzikin jihar ke tsaka mai wuya ga kuma kalubalen tsaro da ke fuskantar jihar domin Bauchi tana tsakiyar shiyyar Arewa Maso Gabas da ke fama da ‘yan Bolo Haram, amma a bisa gogewar Bala Muhammad ya iya shawo kan duk wata kalubalen tsaro. Kuma a yanzu tattalin arzikin Bauchi na ta habaka da ingantuwa, don haka idan ya samu dama zai ninka hakan ga kasar nan.”

Dauda ya kuma kara da cewa Bala Muhammad ya kware wajen iya sarrafa dukiyar al’umman jihar Bauchi, “Wanda ya san Bauchi ko yake ziyarartar Bauchi ya san yadda jihar yake a da baya amma yanzu gwamna mai ci ya samar da ayyukan hanyoyi, kwalbati-kwallbati, asibitoci, azuzuwan karatu, da sauran fanninin bunkasa rayuwar al’umma. Muna da yakinin in ya zama Shugaban kasa Kakarmu za ta yanke saka,” ya shaida.

A bisa haka ne shugaban kungiyar ya roki gwamna Bala Muhammad da ya fito takarar shugaban kasar nan tare da neman ‘yan Nijeriya da su mara masa baya gami da kiransa da ya fito neman wannan kujerar, “Bala ya taka rawar gani a lokacin da yake Ministan Birnin tarayya ya san kasar nan tun a wancan lokacin sosai, kuma ya sake gogewa a fagen mulkin al’umma ga kuma yanzu yadda da yake baiwa kowa mamakin yadda yake sake fasalta Bauchi, tabbas in ya zama shugaban kasa lallai za a samu inganci da nagarta.”

Daga bisani ya nemi jam’iyyar PDP da ta darje ta zakulo nagartacce da ya dace domin ta ba shi tikitin tsayawa takarar shugaban kasar a karkashin jam’iyyar domin talakawa su samu karin aminci da gamsuwa ga jam’iyyar.

- Advertisement -