Ɗan Shugaban kasa Buhari Zai Auri Ƴar Sarkin Bichi

- Advertisement -

Ɗan Shugaban kasa Buhari Zai Auri Ƴar Sarkin Bichi

Ɗan gidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, zai auri ‘ƴar Sarkin Bichi, Zahra Nasir Ado Bayero.

Wata majiya mai tushe ta bayyana wa majiyarmu ta Daily Nigerian cewar, za’a ɗaura Auren ne nan da Watanni 2 zuwa 3 masu zuwa.

Bidiyo: Yanzu Akayi Nasarar Kama Me Sayarwa Da ‘Yan Ta’adda Baburan Hawa Da Tsadar Gaske

Zahra Bayero, wacce a yanzu haka take karatun Digiri a ƙasar Burtaniya, jika ce ga Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Dr. Ado Bayero.

Majiyar ta bayyana cewar, an jinkirta ɗaura Auren ne, saboda Mahaifiyar Angon, wato Aisha Buhari, ta je Birnin Dubai neman lafiya, inda ta shafe watanni 6 a can, kafin daga bisani ta dawo gida Najeriya.

-Majiya Idon Mikiya

- Advertisement -