Ɗan Najeraya mai shekaru 23 ya zo na ɗaya a gasar Al-Qur’ani ta duniya a ƙasar Kenya

0
62

Ɗan Najeraya mai shekaru 23 ya zo na ɗaya a gasar Al-Qur’ani ta duniya a ƙasar Kenya

Dan takara gasar karatu Qur’ani mai wakiltar Najeria mai suna Al-Bashir Goni Usman Goni, mai shekaru 23 yazo na 1 a wurin musabakar Al-Qur’ani mai girma ta duniya wadda aka gudanar a ƙasar Kenya, kuma Al-Bashir shi ne yazo na biyu a wurin musabaƙar Al-Qur’ani ta duniya wadda aka yi a ‘King Faisal Qur’anic Competition’ a kasar Saudiyya, An kammala wannan karatun a jiya Juma’a 12 ga watan Maris 2021.

Matashin ya fito ne daga jihar Borno ya yi karatu a makarantar Center for Higher Qur’anic Memorization For Sheikh Goni Idris Annayim, Maiduguri.

Wuff! Ku Kalli Hotunan Yadda Wannan Dattijon Yayi Wuf Da Wata Kyakykyawar Budurwa

Kuma Mallam Tijjani Auwal Gashu’a da Mallam Umar Umar Bolori sun shaida min cewar Al-Bashir Goni Usman ya haddace Al-Qur’ani mai girma yana ɗan shekara 13 da haihuwa, a cikin malaman sa akwai Mahaifin sa Goni Usman Goni Idris tare da Goni Tahir Goni Idris wanda suka bayyana shi a matsayin haziƙi jajirtacce ko da yaushe ba shi da wani abun yi sai karatun Al-Qur’ani mai girma.

Tuni dai ƴan uwa da sauran al’ummar Najerya suka soma tofa albarkancin bakin su dangane da wannan baiwa ta wakilci, wannan dai ba shi ne karo na farko da Najeriya ke samun nasara walkilci a gasar karatun Al-Qur’ani mai girma a matakin ƙasa da ƙasa ba.

Daga Anas Saminu Ja’en

What's On Your Mind?