Ƴan Boko Haram na can sun kai hari a garinsu Gwamna Zulum a Borno

0
106

Wani rahoto da ba a tabbatar da sahihancinsa ba ya nuna cewa wasu ƴan ta’addan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari Hedkwatar Ƙaramar Hukumar Mafa a Jihar Borno, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Rahoton ya ce yan ta’addan suna can suna musayar wuta da jami’an tsaro.

Ƴan Boko Haram na can sun kai hari a garinsu Gwamna Zulum a Borno

An fatattaki Sarkin Fulanin Oyo da iyalansa daga gidansa, an ƙone motocinsa 11

Arewa maso gabashin Mafa ne garinsu Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum.

Garin na da nisan kimanin kilomita 40 daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce daruruwan mutane suna ta tserewa suna shiga daji domin tsira da ransu a yayin da sojoji ke ƙoƙarin ɗakile harin.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma’aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Day by day Belief ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

What's On Your Mind?